KWANAN nan Ƙungiyar Dattawan Kannywood ta naɗa Farfesa Sule Bello a matsayin shugaban amintattun Gidauniyar (Kannywood Foundation) da aka yi wa rajista. Ba ni kaɗai ba, da yawa waɗanda su ka san wanene Farfesa sun yi murna ganin irin fa’idar da shugabancin nasa zai kawo wa gidauniyar da kuma masana‘antar baki ɗaya. Kwatsam, sai Allah ya karɓe shi a ranar Lahadi, 3 ga Oktoba, 2021.
Kafin shekarar 1987, ɓangaren da ke kula da al’adun gargajiya a gwamnatin Jihar Kano (Kano da Jigawa a yanzu) wani ɗan sashe ne a Ma’aikatar Yaɗa Labarai. A sashen ma, babu abin da ake yi sai kula da harkar rawar ƙoroso. Amma da gwamnan soja na lokacin ya zartar da dokar da ta kafa Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano (History and Culture Bureau, HCB), aka kuma damƙa wa Dakta Sule Bello shugabancin ta, sai al’amuran ta su ka canza.
Masanin tarihin ya duƙufa wajen mayar da sabuwar hukumar ta HCB ta amsa sunan ta na kula da tarihi da kuma inganta al’adun gargajiya ta kowace hanya, musamman ta hanyar ɗaukar nagartattun ma’aikata, a ciki da wajen ma’aikatun gwamnati, ta hanyar ba sani ba sabo, kuma kowa ƙwarewar sa ta kai shi. Ina ɗaya daga cikin su.
A wancan lokaci, ina ɗaya daga cikin ‘yan ƙungiyar wasan kwaikwayo ta ‘Theatre International’ da ke gabatar da wasannin ta da harshen Turanci a ofishin kula da al’adun gargajiya na Birtaniya (British Council) da ke Ƙofar Nassarawa, Kano. Mun kuma je mun gabatar da wani wasa da harshen Turanci da na rubuta, a dandalin wasan kwaikwayo na HCB da ke Sokoto Road. Da labari ya je kunnen shugaban wajen, Sule Bello, sai ya sa shugaban wannan ɓangare, Muhammad Kirikasamma, ya kira ni. Da na je, daga ni sai shi a ofishin sa, cikin hira ya yi min wasu ‘yan tambayoyi kan inda na koyi rubuta wasan kwaikwayo da wasan daɓe, ni kuma na ba shi labarin irin horon da na samu a British Council, Kano, da ƙungiyar wasan kwaikwayo ta ‘NYSC Theatre Group’ a Abuja, da kuma ‘Abuja Theatre Company’ a shekarun 1984 zuwa 1986.
Ni na ɗauka hira kawai mu ka yi da shi ta nishaɗi, tunda yake mutum ne mai sauƙin kai da son jin labarai, ashe intabiyu ce ta ɗaukar aiki!
Da na tafi, ban sake waiwayen hukumar ba sai da aka tafi aka nemo ni da in je in karɓi takardar kama aiki. A lokacin da na je ne aka ce in rubuta takardar neman aikin da ya ba ni.
Kusan irin wannan ce ta sake faruwa a lokacin da ya na shugaban Hukumar Fasaha da Al’adu ta Ƙasa (National Council for Arts and Culture). Farfesan ya shige gaba tare da taimaka wa Sadiq Ɓalewa wajen ɗaukar fim ɗin sa, ‘Ƙasar Mu Ce’, shi da tawagar masu aikin ɗaukar fim ɗin da su ka zo daga Ingila, a wasu jihohin arewacin ƙasar nan. Sule Bello ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙaddamar da fim ɗin a London da kuma nuna shi a wasu wurare a nan gida Nijeriya.
Saboda muhimmancin wannan al’amari a wancan lokaci, sai na sa shi a matsayin babban labari a mujallar ‘Tambari’ da na ke yi wa Edita. Da Farfesa ya zo Kano sai na kai masa ziyara a gida, na kuma nuna masa. Farfesa ya yi murna mutuƙa tare da yaba mana kan wannan ƙoƙari na samar da mujallar da labarin abubuwa irin waɗannan. Ni kuma na yi hakan ne domin ina so ya ɗauke ni aiki a hukumar sa, ganin yadda wasu daga cikin abokan aiki na a HCB su ka koma can wurin sa da aiki a Abuja. Farfesa ya tambaye ni wanda ya ke yi min zane da tsarin mujallar, ya kuma ce ya na son ganin sa.
Kwanaki kaɗan da yin haka, sai na samu takarda daga hukumar NCAC da adireshi na, amma ta Malam Aminu Adamu ce, mai yi min zane. Farfesa ya ɗauke shi aiki, tabbacin cewa ya je ya same shi bayan na isar da saƙo. Wani abin mamaki, hatta jami’an hukumar sa da ke nan Kano ba su san an yi haka ba sai da takardar sa ta fito su ka kawo min.

Daga baya na fahimci cewa Farfesan ya tsallake ni ne saboda kar a ce ya kwashe wa wurin da ya kafa ƙwararrun ma’aikatan sa. Hakan kuwa ya fito ƙarara ne a cikin 1990 a lokacin da shugaban sabuwar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, Mista Ademola James, ya matsa ƙaimi tare da zage damtse wajen hana duk wani fim da bai amsa sunan sa ba shiga kasuwa. Hankalin Mista James a lokacin ya na kan finafinan kudu, mu na arewa ba a maganar mu saboda tsananin lalacewar su a wajen tsari da ɗaukar hoto da sauti da labari, in ban da raye-raye da waƙe-waƙe a salo irin na Indiya.
‘Saki Reshe 2’ shi ne fim na farko da ya tsallake kallon ƙwaƙwaf da ƙwaƙuduba na shugaban da ma’aikatan sa a zaman farko na tantance shi. Wata rana na je wata ziyara ta ƙashin kai na a Abuja, na kuma je NCAC don gaishe da Sule Bello. A nan na ga abin mamaki. Farfesan ya yi min tarba ta musamman tare da gabatar da ni ga manyan jami’an sa da cewa ni ne marubuci kuma daraktan ‘Saki Reshe 2’. Ashe ya na bibiyar duk abin da ake yi. Daga ƙarshe dai, ƙafa da ƙafa Farfesa da kan sa tun daga ofishin sa a hawa na uku ya rako ni har zuwa harabar hukumar, ya na mai alfaharin cewa mun fidda shi kunya.
Masana’antar shirya finafinai ta Kannywood daga ƙungiyoyin wasannin kwaikwayo ta soma. Kuma alhakin yi musu rajista da kula da al’amuran su baki ɗaya na hannun Hukumar Kula da Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano (Kano da Jigawa a yanzu). Sanin muhimmacin basira da ƙwazo da hazaƙa irin na masu wannan baiwa, da kuma yadda za a iya amfani da ita wajen cigaban al’umma, tare da hangen nesa, ta sa Farfasa Sule Bello tare Malam Ali Bature su ka ƙirƙiro bikin baje kolin basira da zayyana da sana’o’in hannu na gargajiya, wato ‘Arts and Crafts Exhibition’, ake kuma yin sa sau uku a shekara.
Ana shirya bikin da kuma gudanar da shi a matakin ‘yan firamare da sakandare da ‘yan makarantun gaba da sakandare, da kuma ƙwararru. A kowane rukuni ana ware mako guda ne don nuna zane-zane da ƙirƙire-ƙirƙire na sana’o’in hannu a matsayin gasa, inda a ƙarshe ake raba kyaututtuka ga waɗanda su ka yi nasara a mataki na ɗaya da na biyu da kuma na uku.
A yayin da ake gudanar waɗannan nan bukukuwa ne, musamman a rukunin ƙwararru, ake kuma gabatar da raye-rayen gargajiya da wasannin kwaikwayo, shi ma a matsayin gasa a tsakanin ƙungiyoyin wasan kwaikwayo na Jihar Kano. Ina ɗaya daga cikin jami’an da ke kula da gasar da ake yi ta wasan kwaikwayo, daga baya kuma aka sauya min aiki zuwa mai ɗaukar hoto a duk lokacin da za yi bikin.
Waɗannan bukukuwa sai su ka zama wani wuri da furodusoshi da daraktoci ke gano sababbin ‘yan wasa da za su sa a shirye-shiryen su na wasan kwaikwayo na gidajen talbijin. Misali, Balarabe Musa Mohammed da Muhammad B. Umar na daga cikin waɗanda gidan talbijin na CTV ya tsamo su a irin wannan biki, ya kuma sa su a shirin sa na ‘Hankaka’ da ya yi matuƙar farin jini.
Nasarar waɗannan bukukuwa ta sa shugaba Sule Bello ya ƙirƙiro majalisar gamayyar ƙungiyoyin wasan kwaikwayo ta Jihar Kano, wato ‘Kano State Drama Groups Council’, da kuma ƙarfafar Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa (Association of Nigerian Authors, ANA), ta hanyar ba su ofis a Gidan Ɗanhausa da kuma sa Habibu Sani jami’i mai kula da al’amuran su a hukumar, ya kuma sa aka ɗauki sakataren gudanarwa, Tijjani Continuity, wanda zai yi aiki da su wajen hadahadar ofis.
“Hakika ba rabo da gwani ba”, inji masu iya magana, “sai dai da wuya a mayar da kamar sa”. Babu shakka, ba wai Kannywood kaɗai ba, al’ummar Jihar Kano baki ɗaya sun yi babban rashi idan mun yi la’akari da irin gudunmawar da Farfesa Sule Bello ya ke shirin bayarwa a wannan sabon muƙami na shugaban amintattun ‘Kannywood Foundation’. Domin har ya sa an sa wakilcin ‘yan masana’antar a cikin kwamitin gwamnati na yadda za a farfaɗo da harkar yawon buɗe ido domin inganta sana’o’in gargajiya da kuma samar da aikin yi. Sai kuma ga shi ta Allah ta kasance.
Amma ni babban abin da ba zan taɓa mantawa ba game da Farfesa Sule Bello shi ne yadda ia lokacin sa ya tsaya kai da fata na sai an katange Dutsen Dala, domin a lokacin ana amfani da jakai ana ɗibar ƙasar ana fita da ita birni da ƙauye. A lokacin babu sukar da Farfesa bai sha ba, har da zargin cewa wai ya na shirin dawo da Tsumburbura ne, amma ya tsaya tsayin daka saboda sanin muhimmancin adana abubuwan tarihi. Bayan ya katange dutsen, ya sa ƙofa ta zamani tare da ɗaukar maigadi da kuma babban jami’i mai kula da wurin. Sannan ya sa aka yi wa dutsen matakala daga ƙasa zuwa sama, ta yadda za a hau cikin sauƙi. Irin wannan gatan ya yi wa karofin Ƙofar Mata mai ɗimbin tarihi.
Allah ya jiƙan sa, ya yi masa rahama, amin.
* Malam Yakubu Liman ƙwararren furodusa ne, marubucin labari kuma darakta a Kannywood