FITACCIYAR jaruma Rahama Sadau ta bayyana farin ciki kan ƙara sanya ta a wani fim ɗin Indiya da za a shirya kwanan nan, har ta sha alwashin za ta nuna ƙwarewa sosai a harkar wasan kwaikwayo a shirin.
A cewar ta, saka ta a wannan fim ɗin ma cikar buri ne, kuma za ta dage ta ba maraɗa kunya.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a ranar 10 ga Satumba, 2021 yadda haziƙar jarumar ta yi aikin ɗaukar wani fim ɗin gumurzu na Indiya mai suna ‘Khuda Haafiz’ kashi na 2, na darakta Faruk Kabir, a Lucknow, babban birnin Jihar Uttar Pradesh da ke Indiya.
A lokacin, ta faɗi cewa fitowar ta a fim ɗin ta kasance cikar buri a gare ta.
To yanzu kuma an sake gayyatar ta tare da wasu ‘yan fim na masana’antar Nollywood domin fitowa a wani sabon fim da za a ɗauka a Indiya nan gaba kaɗan.
Jaruman na Nollywod su ne Richard Mofe Damijo (RMD), Sola Sobowale, da Broda Shaggi.
Sai dai ba a bayyana sunan sabon fim ɗin da za a yi ba.

Wadda ta gayyaci su Rahama zuwa Indiya a wannan karon wata babbar furodusa ce kuma jarumar Bollywood mai suna Hamisha Daryani Ahuja.
Wannan shi ne karo na biyu da furodusar mai kamfanin ‘Forever7 Entertainment’ ta shirya fim tare da ‘yan Nijeriya, na farkon shi ne ‘Namaste Wahala’, wanda ya fito a bara a manhajar Netflix.
Ahuja, wadda kuma darakta ce, ta bayyana cewa ta ji daɗin wancan fim da ta shirya tare da ‘yan Nollywood, shi ya sanya ta sake dawowa ta zaɓi wasu jaruman da za ta yi sabon fim da su, ciki har da Rahama Sadau.
Ta ce, “Ina mamakin a ce har an shekara tun da mu ka saki Namaste Wahala, aka ji mu a duniya! Abin farin ciki ne da na samu damar shirya fim ɗi na na farko kuma na ga ya zagaye duniya. To yanzu kuma ina cike da farin cikin sanar da ku cewa ina nan ina tsara wani sabon aikin, kuma a wannan karon za mu ɗauko ‘yan Nollywood ne zuwa Indiya. Babu shakka wannan aiki zai kasance abin tarihi, kuma na ƙosa in kawo maku shi.
“Za mu yi aiki ne tare da wasu daga cikin jarumai da ‘yan wasan barkwanci da aka fi so a Nijeriya, kuma za mu shirya babban abin nishaɗi wanda za ku yi matuƙar son shi. Akwai babban aiki a gaban mu a ‘yan watanni masu zuwa, kuma zan so in riƙa sanar da ku yadda aikin ke gudana na yadda za mu shirya fim da ya haɗa nahiyoyi. Don Allah ku biyo ni, mu shirya majigin nan tare!”
Daga nan ne ta bayyana sunayen ‘yan wasan guda huɗu da za su tafi Indiya daga Nijeriya don ɗaukar fim ɗin a can.
Yayin da ta ke bayyana sunan Rahama a matsayin ɗaya daga cikin jaruman, furodusar ta ce: “Ina bayyana cewa Rahama Sadau za ta biyo mu zuwa Indiya, kuma ina murna ƙwarai da ganin cewa tare da ita za a yi wannan aikin.
“Da man ina so in samu jarumai daga sassa daban-daban, kuma sai ya kasance Rahama ta dace sosai da wani ɓangare na labarin da na yi amanna da cewa ya na da muhimnanci a raba shi.
“Na ƙosa in ga yadda za ta taka wannan rol ɗin, da kuma yadda za mu nuna inda al’adun Nijeriya da na Indiya su ka haɗu – kamar dai a ce wata irin rawa ce, kuma za ku ga yadda ta kaya.”
Ahuja ta wallafa fostar shelar fim ɗin guda huɗu a Instagram, kowacce na nuna jarumin Nijeriya da ta gayyata zuwa Indiya. A ta Rahama, an buga hoton jarumar sanye shataf da tufafin sari irin na matan Indiya da gwalagwalai, kai ka ce Ba’indiya ce, a gefe kuma ga tutocin Nijeriya da Indiya.
Rahama Sadau ta yi murna da wannan gayyatar, inda ta ɗan hasko tarihin yadda ta ke ƙaunar finafinan Indiya tun ta na ƙarama. Ta ce: “Na girma ina kallon finafinan Bollywood, har ina tunanin da ma a ce ni ma in fito a matsayin jaruma a wani daga cikin su. Ni da ma na sha yin la’akari da yadda al’adar Indiya ta ke yin kama da al’adar da na tashi a cikin ta.
“Lokacin da ni da Hamisha Daryani Ahuja mu ka yi magana kan yiwuwar mu yi aiki tare kan sabon fim ɗin da za ta shirya, na yi farin ciki sosai. Na san dai rol ne wanda zai ƙalubalance ni matuƙa, kuma zai nuna ƙwarewa ta a matsayin ‘yar wasa, kuma na ƙosa in ga mamakin da za mu bayar da wannan fim ɗin!

“Abu mafi muhimmanci shi ne na ƙosa in bayyana aikin a gare ku baki ɗaya ku da ku ka mara mani baya kuma ku ke ƙauna ta tun tashin farko. Zan iya yin wannan aiki, domin ku na tare da ni.
“Ku zo ku taya ni mu yi fim da zai karɓu a duk duniya!
“Uwargida Rah ɗin ku dai za a tafi Indiya! Jama’a kun shirya kuwa?”
Wakilin mu ya ruwaito cewa Rahama Sadau ta shigo Kannywood ne bayan ta shafe tsawon lokaci ta na raye-rayen waƙoƙin Indiya a gidajen biki a Kaduna, inda a kan gayyace ta.
Haka kuma ta na daga cikin jaruman Kannywood ƙalilan da su ke jin yaren Indiyanci.
Comments 1