BABBAR furodusar nan da ke Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), ta bayyana cewa za ta yi amfani da sarautar da aka naɗa ta ta Jakadiyar Matasan Nijeriya ta Arewa wajen gyara rayuwar matasa, musamman ma dai ‘yan fim na masana’antar Kannywood.
Ta yi wannan bayanin ne jim kaɗan bayan an gama yi mata naɗin a yau Juma’a, 20 ga Mayu, 2022 a garin Bichi, Jihar Kano.
Sarkin Samarin Daura kuma shugaban Sarakunan Samarin Nijeriya, Alhaji Sani Uba Daura, shi ne ya naɗa ta sarautar, ita da wasu mutum 11.
Dangane da rawar da sarautar da aka ba ta za ta iya takawa a Kannywood, Lamaj ta ce, “Alhamdu lillahi, kamar yadda ka sani ni furodusa ce a masana’antar, kuma in ka duba masana’antar gaba ɗaya matasa ne. Kuma in aka ce sarakunan matasa ba ana nufin samari ba ne kawai, har da matan, amma kuma ka san namiji shi ne shugaba; duk inda mace ta ke, in dai da namiji, shi ne a gaba. Don haka ina ganin wannan sarauta an taɓo inda na ke da alaƙa da shi.”

Ta ƙara da cewa, “Za mu yi amfani da wannan dama mu ja kunnen yaran mu, musamman kan harkar shaye-shayen nan, da kuma mara ji. Amma dai waɗanda ba su ji a waje sun fi ‘yan industiri yawa; su dai kawai saboda an san su ne tare da sunan da su ka yi. Don haka za mu yi iya ƙoƙarin mu mu ga cewa mun kawo canji a wannan masana’anta.”
An fara naɗin da misalin ƙarfe 10:00 na safe kamar yadda aka tsara, ba tare da ɓata lokaci ba, inda aka riƙa kiran su ɗaya bayan ɗaya ana naɗa su.
Bayan an gama naɗin kuma, nan take aka miƙa masu sandunan su.
Waɗanda aka naɗa su ne:
1. Tahir Sheikh Amin – Talba
2. Alh. Abubakar Mohammed S. Bello – Barade
3. Abdullahi Hassan – Sardauna
4. Hauwa Harun – Gimbiya
5. Shehu Bala – Ɗanmasani
6. Idris Abdullahi Ɗanfodiyo – Jakada
7. Fatima Lamaj – Jakadiyar Matasan Nijeriya
8. Jadda Makinta – Sarkin Yaƙi
9. Zainab Sada – Sarauniyar Matan Katsina
10. Binta Shagamu – Garkuwar Matan Nijeriya
11. Rabi’u Biyora – Dijuma
12. Huraira Maina – Waziriyar Sarauniyar Matan Nijeriya
Bayan an gama naɗin, sai uban gayyar, Sani Uba Daura, ya yi jawabi inda ya jawo hankalin matasa a kan su zama mutane nagari domin su ne ƙashin bayan al’umma, sannan su kama sana’a.
Haka kuma ya yi kira ga waɗanda aka yi wa naɗin da kada su bari naɗin da aka yi masu ya sa su riƙa girman kai, domin wata rana wannan alkyabbar da aka saka masu, jama’a ne za su cire ta su saka mutum a rami idan ya bar duniya.

Ya ƙara da cewa, “Ko ni idan har wannan rawanin zai sa ni girman kai, Allah ya cire min shi, in zauna haka nan.”
Haka kuma ya faɗa wa sababbin sarakunan cewa su ma za su iya naɗa mutanen su. Ai kuwa nan take Lamaj ta ce ta ba Mubarak Sise sarautar Majidaɗin Jakadiyar Matasan Nijeriya, kuma ta naɗa Sani Amalo Sarkin Fada.
A hirar da ta yi da mujallar Fim, Hajiya Lamaj ta yi godiya game da wannan matsayi da ta samu, ta ce, “Ina godiya ga Allah da kuma sarakunan samarin Nijeriya da wannan sarauta da su ka ba ni na Jakadiyar Matasan Nijeriya.
“Haka kuma ina ƙara godiya a gare su da su ka ga cancanta ta, su ka ba ni wannan sarauta.”
Da ta ke bayani a kan masarautar da ta ba ta wannan sarauta, Lamaj ta ce, “Shi Sarkin Samarin Sarkin Daura ne, Alhaji Sani Uba Daura, sannan kuma shi ne ciyaman (na) sarakunan samarin Nijeriya, wanda wakili ne na Sultan na Sokoto da Sarkin Bichi; su ne iyaye na wannan masarauta.”
A game da rashin zuwan ‘yan fim na Kaduna bikin naɗin sosai, Lamaj ta kada baki ta ce, “Ka san Bature na cewa ‘you can force a horse to the river, but you can’t force it to drink the water’. Katin gayyata mun raba shi daidai gwargwado, don haka mutanen da su ka samu zuwa min bikin nan sun fi min yuyuyun da ba su zo ba. Batun gaskiya ne, Abba. Batun in kira mutum ‘personally’ na ce na gayyace shi, wallahi ba zan yi ba. Katin gayyata ne na tura a duk wani ‘platforms’ da ya kamata in tura, in sun zo it’s fine, in ba su zo ba it’s fine.
“Su da ma ‘yan Kano sun fi nuna su na kishi na fiye da ‘yan Kaduna. ‘Yan Kadunan da su ka zo ina godiya a gare su sosai, kuma na san masoya na ne. Babu abin da zan ce masu sai dai in yi masu fatan alheri.
“Ni dai wannan sarauta ba nema na yi ba, cancanta ta sa aka ba ni.”
Da Fim ta tambaye ta abin da za ta ce wa wannan masarauta, sai ta ce, “Allah ya ƙara ɗaukaka wannan Masarauta ta Sarakunan Samari na Nijeriya. Wannan masarauta ta samari, akwai Inyamurai a ciki, akwai Yarbawa a ciki, dukkan jihohi 36 akwai sarakunan su a cikin wannan tafiya, kuma kashi 80 na sarakunan nan sun halarci wannan taron. Babu abin da zan ce masu sai Allah ya ƙara ɗaukaka.”

Manyan mutane da dama sun halarci bikin. Sun haɗa da Alhaji Mahadi Sa’idu Gamagira, Alhassan Kwalle, Dakta A.S. Bello, Nasiru Anchau, Murtala Aniya, Sani Ɗangwari, Abba Muhammad, (wakilin Malam Ibrahim Sheme), Khalid Gamagira, Sani Amalo, Mubarak Sise, Abdulmalik A. Tahir, da wakilan Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeriya (K-WAN), wato Halisa Muhammad, Ladidi Tubeless, Muhibbat Abdulsalam, da Maimuna Ja’en, da sauran jama’a.
Da ya ke ranar Juma’a ce, an yi komai a kan lokaci saboda kada a shiga lokacin sallar Juma’a, aka tashi daga taron da misalin ƙarfe 12:00 na rana.



Allah yataimaki matasa da Yan Nageria bakidaya.