MASANA’ANTAR shirya finafinai ta Kannywood a sashen Kaduna ta shiga farin ciki a wannan rana ta Asabar, 12 ga Maris, 2022 saboda ɗaya daga cikin ‘ya’yan ta da ake ganin ya daɗe bai yi aure ba a yau dai ya yi.
Halliru Ahmad (Ɗanmagyazo) ya na daga cikin ‘yan sahun gaba wajen koyar da rawa a lokacin ɗaukar waƙar fim ko ta siyasa.
Ya haura sama da shekara 25 a industiri. Saboda ya haura shekara 45 a duniya, wasu na ganin cewa tsaran ubangidan shi ne, wato Wassh Waziri Hong.

Amma kuma duk da yawan shekarun sa Ɗanmagyazo bai ɗauki kan shi da girma ba, domin komai ƙanƙantar mutum sai ya aike shi ko’ina ba tare da ya damu ba. Sannan ga shi da ladabi da biyayya ga kowa.
Tsawon lokaci Ɗanmagyazo na shan surutu wurin abokan sana’ar sa cewa ya na cikin ƙannen sa, ‘ya’yan sa da jikokin sa ya ƙi aure, shi kuma ko a jikin sa abin bai damun sa, sai dai ya ce lokaci ne, in Allah ya yarda zai zo.
Tun ana kusan saura wata ɗaya ya fara sanar da jama’a cewa an kusa auren sa.

Ilai kuwa, an ɗaura auren Halliru da sahibar sa Firdausi Abdullahi Musa (Nana) da misalin ƙarfe 2:30 na rana a ƙofar gidan su amaryar da ke Layin Service, a Titin Abuja, Rigasa, Kaduna, a kan sadaki N80,000.
Waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Wassh Waziri Hong, Abdullahi Abbas (Ubangari), Lawandi Wassh, Umar Ɗanhausa, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Ibrahim Saminaka, Sulaiman Justice, Abban Waƙa, Abubakar Hunter, Aminu Haske da Sulaiman Ƙira.

A jiya, an yi bikin Ranar Jarumai (Artists Day) a wani fili da ke Mogadishu Layout, Kaduna.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.