KAMAR kowane ƙarshen shekara, mujallar Fim na kawo maku lissafin hayayyafar da aka yi a Kannywood, kamar yadda ta ke kawo maku jerin mace-mace da aurarrakin da aka yi.
A yau ma ga jerin lissafin ƙaruwar da ‘yan masana’antar daban-daban da su ka samu, kamar yadda mu ka kawo maku cikakken labarin kowace haihuwa da aka yi. Sai mu ce Allah ya raya.
*
Laraba, 23 ga Maris:
Allah ya azurta ɗan ƙwallon Nijeriya Abdullahi Shehu da ɗa namiji. Matar sa, tsohuwar jaruma Naja’atu Muhammad, ta haihu a wani asibiti a Istanbul, a ƙasar Turkiyya. An raɗa wa yaro suna Abdulhameed.
*
Litinin, 11 ga Afrilu:
Alhaji Yerima Shettima ya samu ƙaruwa na ɗa namiji, wanda amaryar sa, tsohuwar jaruma Fati Ladan, ta haifa a wani asibiti da ke Unguwar Rimi, Kaduna. An raɗa wa yaro suna Muhammad Shafi’u (Amir).
*

Juma’a, 5 ga Agusta:
Editan mujallar Fim, Abba Muhammad, ya samu ƙaruwar ‘ya mace, wadda matar sa Jamila Ibrahim Dassi ta haifa a asibitin Vicas Specialist Hospital da ke Unguwar Sarki, Kaduna. An raɗa wa yariya suna Khadija (Fanan).
*
Talata, 13 ga Satumba:
Tsohuwar jaruma Hadiza Maina ta haifi ‘ya mace, a asibitin Ashmed da ke unguwar GRA, Zariya. Mijin ta, Alhaji Lawandi Musa, ya raɗa wa yarinya suna Habiba (Hibba).
*
Asabar, 1 ga Oktoba:
Allah ya azurta darakta Saifullahi Safzor da ‘ya mace, wadda matar sa Khadija ta haifa a asibiti mai suna Al-Munir da ke kusa da NDA a Kaduna. An raɗa wa yarinya suna Amina (Minal).
*
Juma’a, 28 ga Oktoba:
Allah ya albarkaci mawaƙi Sulaiman Farfesan Waƙa da ‘ya mace. Matar sa, Sadiya Adamu, ta haihu a gidan Farfesa da ke unguwar Darmanawa, Kano. An raɗa wa jaririya suna Maryam (Princess Mama).
*

Asabar, 10 ga Disamba:
Allah ya azurta mai kwalliya a Kannywood, Mansur Makeup, da ‘ya mace, wadda matar sa, Amina Murtala, ta haifa a asibitin Faris Hospital and Maternity da ke Titin Swimming Pool, Shooting Range, Kabalan Doki, Kaduna. An raɗa wa yarinya suna Maimunatu (Afreen).
![]()






