KULLU nafsin za’ikatil mauti, cewar Allah (s.w.t.) a cikin Alƙur’ani. Wato kowane rai sai ya ɗanɗani mutuwa. Allahu Akbar! Haka mu ka ga ya na faruwa a kullum.
Mutuwa ba ta bar Kannywood ba a cikin wannan shekara mai ƙarewa. Kuma kamar kowace shekara mujallar na kawo maku jerin rashe-rashen da aka yi a Kannywood.
A bana ma mun waiwaya baya, ga lissafin jerin mace-macen da aka yi mun kawo maku domin mu yi juyayi a kai, mu yi addu’ar Allah ya jiƙan su.
MUTUWA
*
Asabar, 26 ga Maris:
Allah ya ɗauki ran ‘ya’yan jarumi Alhaji Balarabe Jaji su huɗu sanadiyyar haɗarin mota a kan hanyar su ta komawa Jaji daga garin Kaduna. Mamatan su ne Maryam, Binta, Sa’adatu da Sulaiman.
*
Talata, 4 ga Afrilu:
Alhaji Muhammadu Gidaje, mahaifin ‘yan fim ɗin nan Yusuf M. Gidaje, Sabi’u M. Gidaje, Haruna M. Gidaje da Nafi’u M. Gidaje, ya rasu a gidan sa da ke Kwanar Lami Filato, Tudun Wada, Kaduna.
*
Talata, 4 ga Afrilu:
Malam Hassan Umar, mahaifin jarumi Mukhtar Hassan SS, ya rasu a gidan sa mai lamba 132 da ke tawayen masallaci, Sabon Layi, unguwar Jushi, Zariya.
*

Lahadi, 10 ga Afrilu:
Allah ya ɗauki ran ɗan mawaƙi Abubakar Yarima, Muhammad Sani, wanda ya rasu sanadiyar shiga Kogin Kaduna.
*
Lahadi, 26 ga Yuni:
Allah ya ɗauki ran ‘yar tsohon shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Murtala Muhammad Aniya, Fatieha Murtala Aniya, wadda ta rasu a Asibitin Mu’awuya da ke Tudun Nufawa, Kaduna.
*
Lahadi, 3 ga Yuli:
Allah ya ɗauki ran daraktan Nura Mustapha Waye. Ya rasu a gidan sa da ke unguwar Goron Dutse, Kano.
*
Alhamis, 28 ga Yuli:
Allah ya ɗauki ran Aisha ‘yar ɗan jarida kuma tsohon furodusa a Kannywood, Salisu Umar Salinga. Ta rasu a gidan mahaifin ta da ke Titin Shehu Idris, Kabala Road, Sabon Gari, Kaduna.
*
Litinin, 22 ga Agusta:
Hajiya Hannatu Yahaya, matar babban furodusa, Alhaji Magaji Sulaiman, ta rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, Zariya.
*
Lahadi, 4 ga Satumba:
Hajiya Safiya Hussaini Sabo, mahaifiyar mawaƙi Abdul Tynkin Maigashi, ta rasu a asibiti mai suna Oshegba Hospital a garin Lafiya, Jihar Nassarawa.
*
Talata, 27 ga Satumba:
Allah ya ɗauki ran jarumi Alhaji Umar Yahaya Malumfashi, a asibiti mai suna Pinnacle Special Hospital, Kano.
*
Juma’a, 30 da Satumba:
Hajiya Hafsa Ahmad, mahaifiyar mawaƙi Ishe Baba, ta rasu a gidan ta da ke Nassarawa, Jos, Jihar Filato.
*
Jama’a, 14 ga Oktoba:
Hajiya Rabi’atu Usman, mahaifiyar jarumi Malam Tijjani Faraga, ta rasu a gidan ta da ke Unguwar Rogo cikin garin Jos, Jihar Filato.
*

Laraba, 23 Nuwamba:
Allah ya ɗauki ran jarumin barkwanci Malam Sa’idu Ado Gano (Bawo) a gidan sa da ke Gano, Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano.
*
Lahadi, 4 ga Disamba:
Allah ya ɗauki ran Mubarak, ɗan furodusa, Magaji Sulaiman. Ya rasu a Kogin Kaduna.

