Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Fim (MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta yi zama da Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin tattauna yadda za a wayar da kan al’umma a game da illar sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi.
Taron wanda ya gudana a ranar alhamis an yi shi ne a ofishin MOPPAN dake Ƙofar Dukawuya kan titin BUK a cikin garin Kano.
Tun da farko da yake jawabi a game da zuwan nasu ofishin MOPPAN ɗin, Kwamanda mai kula da ƙananan hukumomin Fagge, Nassarawa da Ungogo dake cikin ƙwaryar Kano, Sani Musa Bakori, ya ce “A matsayin ku na ‘yan fim masu wayar da kan al’umma, kuna da rawar da za ku taka wajen taimaka wa hukumar wajen yaƙi da shaye shayen da ake yi da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi.”
Ya ci gaba da cewa, “A matsayina na wanda ya karanci harkar sadarwa, kuma na san tasirin midiya a cikin al’umma, don haka abu ne mai sauƙi masu shirya fim su isar da duk wani saƙo da ake so jama’a su gani su fahimta.
“Don haka a wannan zama da za mu yi, zan ɗauki duk wani abu da muka tattauna a rubuce na kai wa magabatana na jiha da na ƙasa domin su ga irin gudummawa da ita wannan masana’anta take bayarwa. Kuma ƙofar mu a buɗe take a gare ku ga duk wani da yake so zai shirya fim ko zai yi wani rubutu a kan wani abu da ya shafi harkar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
“Ana iya zuwa a same mu kai tsaye don mu bayar da shawarwari, domin a riƙa yin su daidai. Idan ma ta kama a gayyato mu mu zo wajen da ake gudanar da aikin don nuna yadda ya kamata a yi aikin, duk za mu bada damar hakan.”
Da yake mayar da martani, Shugaban MOPPAN, reshen Jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, M.O.N, ya ce sun ji daɗin wannan zama na kyautata alaƙar aiki, duk da yake wannan ba shi ne karo na farko da ƙungiyar ta fara zama da hukumar ba, amma sun ji daɗin wannan zaman.
Ya ci gaba da cewa “A baya Shugaban Hukumar na Ƙasa, Buba Marwa, ya taɓa zuwa an yi zama da MOPPAN ta ƙasa, a lokacin Dakta Ahmad Sarari yana Shugaban ta na Ƙasa.
Amma dai abin da mu masu shirya fim muke fuskanta, sau da yawa idan ka zo ka ce za ka yi fim na tallan wani abu daban, to kai tsaye mutane za su gane su ce talla ne kake yi wa wani ko wata ƙungiyar, ko yaɗa wata manufa.
“To sai ka ga idan ka yi shi don kasuwa, sai ya zama mutane ba su cika damuwa da saƙon ba. Saboda haka, hukumomin da abin ya shafa suna ɗan bada wani tallafi wanda zai zama kai ma ka bayar da taka gudummawa, su ma su bayar, tun da kai mai sana’a, a matsayin ka na ɗan ƙasa ko ɗan jiha, idan ka ga wani abu da ake yi na karya doka ko lalata tarbiyya, ko ba a baka kuɗi ba za ka yi iya bakin ƙoƙarin ka don ka ga yadda za ka yi ka hana, matuƙar dai kai ba dillalin abin bane da ba ka so a daina.
“Don haka muka kira ita wannan hukumar da idan ta ga an yi wani fim da ta ga ya dace tare da yin tallan ayyukan hukumar kai tsaye, ko ya nuna wasu abubuwa, to ya kamata a ɗan samu wani abu a dan bayar na nuna wannan fim ɗin an yaba dashi, ga ɗan wani abu. Wannan zai sa mutane su riƙa ƙoƙarin sassakawa, tun da ba za a ce sai an zo an zauna an yi fim gaba ɗaya wanda hukumar ce za ta ɗauki nauyi ba. Ta haka ne za a samu kawo hanyar gyaran da ake fata,” inji Ado Ahmad Gidan Dabino.