FITACCEN mai tacewa da kuma gyara hotunan bidiyo a Kannywood, Abdul’aziz Ezet, ya bayyana cewa ɓacin rai ne ya tilasta masa tsunduma cikin aikin editin sakamakon irin wulaƙancin da ya fuskanta a zamanin da ya ke furodusa.
Matashin, wanda sunan sa Abdul’aziz Abubakar, ya faɗa wa mujallar Fim cewa shi haifaffen cikin birnin Kano ne kuma ya yi makarantar firamare ta Ɗorayi, da makarantar sakandare ta Goron Dutse da ke Ƙofar Famfo, a Kano. Daga nan ya dangana zuwa Kwalejin Horas da Malamai ta Tarayya (FCE), Kano, inda ya samu shaidar malanta.
A kan yadda aka yi ya shiga harkar fim, Ezet ya ce, “Na fara harkar Kannywood tun shekarar 2004 ta dalilin wani aboki na mai suna Hamisu Muchu, kuma na fara da shirya finafinan barkwanci a wannan lokacin, wanda kuma daga baya na canza akalar zuwa harkar tacewa da gyara hoto.
“Hakan kuma ya biyo bayan ɓacin rai da masu gyara hoton su ke sa ni yayin da na kai musu aiki na na gyara hoto. Ganin haka ya sa na yanke shawarar koyon aikin saboda in dinga yi wa kai na, ba sai na zauna ana ɓatan rai ba.
“Kuma a lokacin na yi sa’a duk abokai na ne masu tace hoton. Ashe da rabon shi ne hanyar cin abinci na!”
Ezet ya ce ya fuskanci ƙalubale yayin da ya ke koyon editin, musamman yadda ya haɗa karatun sa da koyon tace hoto. “Mutum ya haɗa makaranta da kuma sana’a, musamman ma ka na ganin ba kuɗi ka ke samu ba, kawai dai sana’a ka ke koya, nan kuma ilimi ka ke nema, dole mutum sai ya yi haƙuri da rashin wadatuwa har ma da lokacin ka, kafin na samu nasara har ma wasu su ke amfana da abin da na samu,” inji shi.
Bugu da ƙari, ƙwararren editan ya yi tsokaci kan yadda cigaban kimiyya ke shafar irin aikin su na tacewa da haɗa hoto, ya ce: “Yanzu fa duniya ta sauya da kuma yanayin yadda ta ke sauri. Ma’ana, akwai yanzu abubuwan da su ka yi mana nisa kuma mu ke buƙatar mu same su, amma sai ka ga mutum bai da jarin da zai mallaki wannan abu. Wannan abu kuwa ba komai ba ne illa sauyin zamani wanda a yanzu akwai kamfutar da ake gyaran hoto da ita ta sama da (naira) miliyan takwas, da ma ta miliyan goma a ƙasashen duniya, mu kuma a maganar gaskiya ba mu da halin sayen irin waɗannan abubuwan.”
Maganin matsalar, inji shi, shi ne “gwamnati ta shigo harkar nan ka’in da na’in, duba da yadda a yanzu masana’antar tamu ta ke ƙara farfaɗowa kamar yadda mu ke ganin cewa wannan sana’ar tamu yanzu mu ke sa ran za mu fara samun manyan kuɗaɗen da za mu iya rayuwa da su.
“Kamar yadda mu ke kallo, za ka ga gwamnati a wata ƙasar, musamman ƙasar Indiya wacce mu ke kwaikwaya, wani fim ɗin ma da za a ɗauko shi shi ne ma kasafin kuɗin wata jahar, wanda kuma ya samo asali ne sakamakon yadda gwamnatocin su su ke ba su gudunmawa ɗari bisa ɗari.
“Kuma da za a aiwatar da haka a wannan ƙasa, to da harkar tamu ta samu tagomashi mara misaltuwa.”
Duk da ƙalubalen da sana’ar ke fuskanta, Abdul’aziz Ezet ya na cike da hamdala da godiya da Allah saboda nasarorin da ya samu a harkar. Ya ce, “Ba zan taɓa mantawa da irin abubuwan alkhairi a wannan sana’a tawa ta gyara hoto ba. Ba abin da zan ce da Allah sai godiya, saboda na samu nasarori da dama.
“Babbar nasara ita ce na samu damar gina gida da wannan sana’ar tawa, sannan na yi aure. Da ita na ke riƙe iyali na. Kuma duk wasu ayyuka na na yau da kullum na rayuwa, da wannan sana’ar tawa na ke yi. Ka ga kuwa duk abin da zai ba ka ci da sha na yau da gobe a cikin sa ai ka gama samun babbar nasara.
“Kuma ta dalilin wannan sana’ar tawa mutane da dama sun san ni, kuma ina da alfarma da yawa dalilin ta.”
Wata nasarar da mujallar Fim ta gani a tare da Ezet ita ce sama da shekara takwas Abdul’aziz Ezet ya mallaki kamfanin sa na kan sa wanda a ƙarƙashin sa ya ke ɗauke da mutane sama da bakwai masu koyon aikin editin da ma ɗora fassara a kan fim, wato ‘subtitle’.
Finafinan da Ezet ya tace sun haɗa da ‘Umarnin Uwa’, ‘Da Kishiyar Gida’, ‘Rashin Masoyi’, ‘Rarrashi Na’, ”Yar Aiki’, ‘Alkuki’, ‘Zawarawa’, ”Ya Daga Allah’, da kuma shahararren fim ɗin nan mai dogon zango wanda tashar talbijin ta Arewa24 ta ke haskawa mai suna ‘Labari Na’.

A hirar sa da mujallar Fim, akwai wani muhimmin kira da Ezet ya yi ga matasa ‘yan’uwan sa, musamman na arewacin Nijeriya, inda ya ce masu: “Babbar matsalar da mu matasa mu ke fuskanta ita ce yawancin matasan mu ba sa tunanin ya goben su za ta kasance. Sannan sun raina kan su ta yadda matashi wai zai buɗi baki ya ce shi fa ba ma ya sa kayan sa na gargajiya, wato manyan kaya, wanda kuma tun daga haka matashi ya raina kan sa.
“Shi ya sa ko da sun manyanta ko sun zama ‘yan siyasa za ka ga waɗanda su ke tare da su, wato masu yi musu hidima, ba namu ba ne ba, tunda mu mutanen mu ba sa burge su; da ma mun raina kan mu.
“Ya kamata matasa su farka kuma su fara gane cewa a wacce al’umma mu ke; mu Hausawa ne kuma duk duniya ba mu da abin da ya wuce Hausa.
“Sannan dole sai mun bi tarbiyyar al’ummar mu da al’adun mu, kuma sai mun yi haƙuri mun jure kuma mun nema.”
Abdul’aziz Ezet ya ƙara da cewa, “Mutanen da matasan mu su ke kallon rayuwar su kuma su ke kwaikwayowa ba shi ne abin da ya dace su yi ba. Ya kamata su gane duk kakannin mu da su ka yi nasara a rayuwa wasu sun riƙe noman auduga, wasu saƙa, rini, da sauran su. Kamata ya yi su gane dole fa sai matashi ya gane ga fa hanyar da ake bi a yi nasara. Kar ya kasance kullum tunanin su mafarki ne kamar yadda za ka ga kullum su tunanin su kawai ya za a yi su sa kaya manya masu tsada, wanda kuma hakan kan sa su manta da abin da ya ke a gaban su, musamman rayuwar su ta gaba.”
Lallai wannan matashi jan gwarzo ne, mai kyakkyawar alƙibla, wanda ya dace sauran matasa su yi koyi da jajircewar sa. Da fatan za su farga su gane.
![]()







