ƁARAYI masu garkuwa da mutane sun sako iyalin wani shahararren mai taimaka wa ‘yan fim a Jihar Zamfara, Alhaji Babangida Damɓa, kwanaki uku bayan sun kama su a cikin gidan su.
Da misalin ƙarfe 12:00 na daren ranar Talatu, 10 ga Agusta, 2021, ɓarayin su ka kutsa kai cikin gidan Babangida, su ka yi harbe-harbe, har su ka harbe shi, sannan su ka yi awon gaba da matar sa da ɗan ta mai shan nono.
Ba su sako su ba sai a yau.
Ɗaya daga cikin jagororin harkar fim a Zamfara, Alhaji Ali Bulala Gusau, ya sanar da cewa Allah ya kubutar da uwa da ɗan ne bayan an biya kuɗin fansa.

Tun washegarin ranar sace mutanen, Ali Bulala ya yi addu’a kamar haka: “Allah ka yi muna mafita a Zamfara. Gida ba ka tsira ba, a wjen ma ba ka tsira ba! Mu na neman addu’ar ku ga wannan masoyin Kannywood Allah ya yi wa iyalin shi mafita.”
Idan kun tuna, shi ma Ali Bulala kwanan nan ɓarayi su ka sace shi a hanyar Gusau zuwa Sakkwato, kuma ba su sako shi ba sai da ‘yan’uwan sa su ka biya diyyar naira miliyan biyar.
Halin rashin tsaro sai ƙara ta’azzara ya ke yi a yankin arewa-maso-yamma na Nijeriya, inda a kullum daga ka ji an sace wannan sai an kashe wannan ko an kai wa gari kaza hari an tafka ta’asa.
