BABBAN furodusa a Kannywood, Alhaji Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe), ya yi barazanar zai maka jarumi Abdallah Amdaz a kotu bisa zargin aikata laifukan ɓata suna a kan ‘yan fim da ya ce ya yi.
Idan kun tuna, Amdaz ya yi munanan kalamai a kan masana’antar shirya finafinan inda ya ce da yawa daga cikin ‘yan fim mazinata ne.
Ya yi kalaman ne a gaban shugabannin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, lokacin da hukumar ta gayyaci ‘yan fim da su bayyana a gaban ta.
‘Yan fim da dama sun harzuƙa da maganganun da Amdaz ya yi.
Alhaji Sheshe ya umurci lauyoyin sa da su fara shirin maka Amdaz a kotun a bisa zargin ɓata suna da ya ce ya yi masa da sauran ‘yan Kannywood.
Lauyoyin da Alhaji ya ɗauka daga kamfanin ‘N & N Attorneys’, su na da ofisoshi a Legas da Abuja. Amma ba a nuna ko su na da ofis a Kano ba.
Takardar da lauyoyin su ka tura wa Amdaz ta na ɗauke da sa-hannun lauyoyi uku, wato
Cif Nnamdi Anana da Mista Nkiru Joseph da kuma M.I. Baba.

Takardar barazanar da lauyoyin Alhaji Sheshe su ka aika wa da Amdaz
Mujallar Fim ta fassara takardar kamar haka: “1. Ka yi la’akari da cewa wanda mu ke wakilta ya na daga cikin manyan furodusoshin da ake girmamawa a Kannywood, kuma ya na da ƙima a idon iyalan sa da abokan sa da dubban masu biye da shi, kuma ya yi fice a ciki da wajen ƙasar nan.
“2. Haka kuma wanda mu ke wakilta ya na zaman lafiya da abokan aikin sa kuma ba a taɓa kama shi da wata ɗabi’a ta assha ko rashin ɗa’a ba a duk tsawon lokacin da ya ke zaune a cikin Kannywood.
“3. Sannan abin matuƙar al’ajabi ne ga wanda mu ke wakilta, duk da ɗimbin kyakkyawar gudunmawar da ya bayar ga Kannywood da kuma jama’ar Musulmi Hausawa, sai kai ɗin nan a wajen wani jawabi da ka yi a gaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ka yi wasu kalamai na ɓatanci da rashin tunani a kan mutuncin fitattun furodusoshi da daraktoci da jarumai na Kannywood, waɗanda wanda mu ke wakilta ya na ɗaya daga cikin su.
“4. Kuma waɗannan maganganun da ka yi sun zubar da mutunci da ƙimar wanda mu ke wakilta a idon duniya, musamman masoyan da sauran jama’ar da ya ke zaune a cikin su.
“A bisa waɗannan abubuwan da ke sama ne mu ka rubuto maka wannan takarda a madadin wanda mu ke wakilta domin mu BUƘACE KA da ka fito ƙarara a idon duniya ka janye maganganun ka da ka yi ko kuma ka ɗauki zaɓin cire wanda mu ke wakilta daga cikin jerin sunayen miyagun da ka faɗa, a cikin awa ashirin da huɗu (24) daga ranar da ka karɓi wannan takardar, amma idan har ka ƙi to za mu kammala shirin aiwatar da umarnin da wanda mu ke wakilta ya bayar na ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakin shari’a a kan ka.
“Mu na fatan za ka ɗauki shawara ka yi abin da ya kamata don kauce wa ƙara kan aikata babban laifi da ka yi.”
Ɗimbin mutane sun shiga tattaunawa kan wannan barazana da Alhaji Sheshe ya yi tun daga lokacin da ya wallafa takardar lauyoyin a soshiyal midiya. A yayin da wasu ke yabon furodusan, wasu kuwa cewa su ke ai gaskiya ce Amdaz ya faɗi.
Sai dai wakilin mujallar Fim ya lura da cewa takardar lauyoyin na ɗauke da kuskuren kwanan wata da ya nuna cewa an rubuta ta ne a ranar 16 ga Fabrairu maimakon watan Nuwamba.