A CIKIN ‘yan kwanakin nan wata ji-ta-ji-ta a ta yi ta yaɗuwa a soshiyal midiya, musamman a wasu shafuka na TikTok, game da fitaccen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (Ala), wai ya rasu, har ma wasu suka ɗauka kamar da gaske ne.
Sai dai duk yadda aka kai ga yaɗa labarin, abin da mutane da dama suke faɗa shi ne me ya sa ba a samu labarin a wasu jaridu ba sai a TikTok?
A kan wannan labarin dai mai kama da almara mujallar Fim ta nemi jin ta bakin Ala, inda ta tambaye shi idan ya samu labarin da ake yaɗawa.
Ala ya ce, “Gaskiya ne labarin ya yaɗu sosai, don ni ban gan shi ba ma sai daga baya. Amma dai abin da na fara ji da farko shi ne kiran waya daga sassan duniya babu ƙaƙƙautawa da ɗimbin masoya suke yi mini, kuma a duk lokacin da na ɗaga wayar sai kawai na ji an ce, ‘Ala, yanzu muke ganin labarin cewar Allah ya yi maka rasuwa.’
“Ni kuma sai na ce, ‘To ai ga ni muna magana da kai, don haka ba gaskiya ba ne.’
“Kuma wannan labarin ya yi matuƙar ba ni mamaki saboda mutane sun ɗauki labarin da muhimmanci, amma dai daga sun kira ni mun yi magana sai su tabbatar ba gaskiya ba ne.”
Ala ya ci gaba da cewa, “Shi irin wannan yaɗa labaran na mutuwar wani ɗan fim ko mawaƙi ba wani sabon abu ba ne, don haka jama’a su rin}a tantance wajen samun labari mai inganci, domin idan mutane sun lura babu wata babbar kafar ya]a labarai da ta yi fice a duniya kuma take da rajista da ta sanar da wannan labarin.
“Kuma shi labarin mutuwa ta za a same shi ne daga wajen wani makusanci na ta hanyar kafar yaɗa labarai mai inganci.
“Don haka mutane su gane su masu yaɗa irin wannan labarin wasu irin mutane ne da ba su damu da mutuncin su ba da ko ƙimar aikin da suke yi ba, don haka a ƙoƙarin samar wa kan su mabiya za su iya ƙirƙirar labarin ƙarya a kan kowa, ba su damu da mutuncin su ba, su kawai buƙatar su ta son zuciyar su ce a gaban su.”
![]()







