TSOHUWAR jarumar Kannywood, Hajiya Halisa Muhammad, ta bayyana yadda ta ce wani mutum ya damfare ta maƙudan kuɗaɗe.
Halisa ta bayyana a Facebook a daren jiya Lahadi cewa, “Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Suna na Halisa Muhammed,
mai fama da ciwon kansar mama (breast cancer).
“Ina rubuta wannan wasiƙa ne da zuciya mai rauni da tausayi, ina neman adalci daga al’umma, ’yan sanda, da gwamnatin Jihar Kano, da dukkan masu riƙe da madafun iko.
Ta ce, “Ni baiwar Allah ce mai fama da ciwon kansar mama da ke buƙatar duba lafiya ta a ƙasashen waje. Kuma na dace mai girma gwamnan Jihar Kano ya ɗauki nauyin yi mun allurai da magunguna.
“A cikin wannan hali na, wani bawan Allah mai suna Bashir Abdullahi ya karɓi kuɗi na har naira miliyan bakwai da dubu ɗari biyar (N7,500,000) da sunan zai taimaka min da wani asibiti da ke Madina a ƙasar Saudi Arabia wajen yin visa zuwa asibitin domin jinya.
“Amma abin takaici, bayan ya karɓi kuɗin, ya yi min visa na bogi kafin mu tafi, ya ba ni tikitin shi ma na bogi, na yi sallama da gida na tafi filin jirgi, aka ce min babu suna na a jerin masu tafiya.”
Halisa ta ci gaba da cewa, “Wannan abu ya jefa ni cikin babban raɗaɗi da damuwa, ba wai na rasa kuɗi kawai ba, har ma da lafiya ta da rayuwa take cikin haɗari.
“Ina roƙon ‘yan sanda, gwamnati da al’umma masu adalci da su taimaka a bi mani hakki na, a binciki lamarin, a kuma tilasta masa mayar min da kuɗi na. Rayuwa ta tana cikin haɗari. Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un.
“Don Allah ku taimaka mani yadda kuka saba taimakawa saƙon ya isa inda ya kamata ya je.”
![]()







