ZA a ɗaura auren jarumin Kannywood, Jamilu Adamu Ɗan Bayaro, wanda aka fi sani da Kochila, a jibi Asabar a Kaduna.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa Sa’adatu Nuhu da ƙarfe 1:00 na ranar, a Masallacin Juma’a Sultan Bello da ke Unguwar Sarkin Musulmi.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Kochila yana ɗaya daga cikin ‘yan fim da ake yi masu tsiya da cewa sun ƙi yin aure, wanda har aminin sa Adam A. Zango ya sha tsokanar sa a kai a soshiyal midiya.
Sai dai jarumin bai taɓa damuwa da surutan da ake yi masa ba.
Wakilin mujallar Fim ya taɓa tambayar sa game da aure, sai ya ce, “Aure lokaci ne, muna nan muna jiran lokacin da Allah ya tsara mana.”
Kochila ya nemi addu’a daga duk wanda bai samu damar halartar ɗaurin auren ba.
![]()







