A YAU Asabar, aka ɗaura auren jarumin Kannywood, Jamilu Adamu Ɗan Bayaro (Kochila) da sahibar sa Sa’adatu Nuhu.
An ɗaura auren a Masallacin Juma’a na Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna, ji kaɗan bayan an idar sallar azahar, a kan sadaki N200,000.

Shugaban Northern Stakeholders Initiative (NSI) kuma fitaccen ɗan gwagwarmaya, Alhaji Yerima Shettima, shi ne wanda ya wakilci Adamu Kochila, ya karɓi auren.
Manyan mutane da ‘yan fim daga sassa daban-daban da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Dakta Ali Nuhu, Alhaji Nastura Ashir Shariff, Abdul Amart, Sadiqu Artiste, Ɗayyab Hassan Maiɗa’a da Kabiru A. Zango.

Bayan ɗaurin auren an yi walima a wurin shaƙatawa na Syde Resort da ke Titin Raɓah, Malali, Kaduna.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
![]()







