• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, May 31, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ɗan’uwa ko ka taɓa jin labarin Ambasada John Mamman Garba?

by DAGA 'NIGERIAN BAHAUSHE'
August 12, 2022
in Rayuwa
0
Ambasada John Mamman Garba

Ambasada John Mamman Garba

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SUNAN sa John Mamman. Sunan mahaifin sa Garba Katsina. Kakannin sa sun riƙe sarautar Ƙauran Katsina kafin lokacin Jihadi. 

Shi ne ɗan Arewa na farko da ya karanci ilimin tattalin arzikin ƙasa, wato ‘Economics’. Ya samu digirin sa na ‘Economics’ ne daga ƙasaitacciyar makarantar nan da ake kira ‘London School of Economics’.

Shi ne ɗan Nijeriya na farko da ya riƙe muƙamin ‘Executive Director’ a Bankin Duniya (World Bank) da ke birnin Washington, DC.

Ya na cikin ma’aikatan farko na Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Wajen Nijeriya tun sa’ilin da aka buɗe ta a shekarar 1950.

Shi ne ya fara buɗe ofishin jakadancin Nijeriya da ke Amurka. Ya na Amurka a lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba, 1960, a nan su ka yi walimar murnar samun ‘yanci.

John Mamman Garba ya riƙe muƙamin Ambasadan Nijeriya a ƙasashe biyar – Amurka da Italiya da Girka da Cyprus da Andalus (Spain).

Kamar yadda mu ka sha faɗi mu na nanatawa, a ƙasar nan kullum so ake a nuna Bahaushe bai isa ba. Duk inda Bahaushe ya yi fice, ko dai a kore masa hausancin sa ko a naƙasa asalin sa ko kuwa a yi ƙoƙarin binne tarihin sa. 

An yi ƙoƙarin binne tarihin Ambasada John Mamman Garba.

Littafin ‘Time Has Come…’ na Ambasada John Mamman Garba

Ba titi ko layi ko gini ko cibiyar nazari ko ɗakin karatu da sauran su da aka sanya wa sunan sa don tunawa da shi. 

Mun san mafi yawancin masu karatun wannan rubutun sai yanzu su ka fara jin sunan wannan bawan Allah. 

Amma Allah cikin ikon sa, ya ba Ambasada Mamman Garba damar rubuta tarihin rayuwar sa da kan sa cikin wani littafi mai shafi kusan 400 da ya sa wa suna ‘The Time Has Come…’, wanda kamfanin wallafa littattafai na Spectrum ya buga. 

Ambasada Mamman Garba ya koma ga mahaliccin sa a shekarar 1989 kafin littafin da ya rubuta ya fito daga ɗab’i, ya na da shekaru 70 a duniya. Akwai ‘ya’ya da jikokin sa a Wusasa ta Zariya inda ya yi rayuwar sa.

Mu na alfahari da Ambasada John Mamman Garba.

© Nigerian Bahaushe

Loading

Tags: Bankin DuniyaJohn Mamman GarbaKatsinaƘauran KatsinaLondon School of EconomicsNigerian ambassadorNigerian IndependenceSokoto JihadSpectrum PublishersThe Time Has Come...World BankWusasaZariya
Previous Post

Cikar buri ne da na fara samun ‘ya mace – Abba Mujallar Fim

Next Post

Ni ba ɗan maula ba ne a harkar fim, inji Aminu Baba Ari

Related Posts

Mace na yin wanki (Hoto daga: Deposit Photos)
Rayuwa

Zamantakewa: Tsakanin darajar namiji da mace

July 11, 2023
Tsohuwar da ke buƙatar taimako
Rayuwa

In da ran ka…!

June 13, 2022
Ibrahim Kabir Magaji (Ibee Graphics)... yadda ya zana kan sa da komfuta
Rayuwa

Abin da ya sa na ke zana hotunan ‘yan Kannywood – Ibrahim Kabir Magaji

September 27, 2021
Alfanun albasa ga lafiyar jiki
Rayuwa

Alfanun albasa ga lafiyar jiki

September 7, 2021
Tsakanin shahara da jarraba
Rayuwa

Tsakanin shahara da jarraba

April 5, 2021
Matsalar almajirai ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Arewa
Addini

Mu dai a Arewa an sha mu mun warke!

October 2, 2019
Next Post
Aminu Baba Ari

Ni ba ɗan maula ba ne a harkar fim, inji Aminu Baba Ari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!