DA azahar a yau aka yi jana’izar shugaban kamfanin Birniwa Concept, Alhaji Mu’azu Muhammad Birniwa, wanda aka fi sani da El-Mu’az Birniwa, wanda ya rasu a daren jiya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa El-Mu’az Birniwa ya rasu ne a filin wasan ƙwallon bikin abokin aikin sa, mawaƙi Auta Waziri, bayan zuciyar sa ta buga, ana tsakar buga ƙwallo ya yanke jiki ya faɗi a jiya Laraba, 4 ga Disamba, 2024.
Shekarun sa kimanin 43 a duniya.
Marigayin ya rasu ya bar mahaifiyar sa, da mata biyu da ‘ya’ya shida – mata uku, maza uku.
An yi masa sallah a bayan sallar azahar a masallacin Alhaji Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji (NDC) da ke kan titin zuwa Zariya.
Daga nan aka wuce da shi gidan sa na gaskiya a maƙabartar unguwar.

Jama’a daga ɓangarorin da dama na Arewacin Nijeriya sun halarci jana’izar, har ya kasance a masallacin maza da mata sun cika shi babu masaka tsinke.
Cikin waɗanda suka halarci jana’izar har da ɗan majalisa mai wakiltar Mazaɓar Igabi ta Yamma a Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, Honorabul Yusuf I. Zailani, da Malam Abubakar Goron Namaye, da ‘yan fim irin su Abdul Amart, Aminu Saira, Falalu Ɗorayi, Ibrahim Maishunku, Nuhu Abdullahi, da Nazifi Asnanic.

Wasu ‘yan fim ɗin kuma su ne Alfazazee Muhammad, Sulaiman Sir Zeesu, Musa Mairabo, Ɗayyab Mai Ɗa’a, Umar Big Show, Auta Waziri, Ikhram Kano, Ali Jita, Jamilu Ɗan Masu Kuɗi, Ibrahim Birniwa, Sani Kwarko, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Sagir Baban Kausar, Abdullahi Abbas Abdullahi Abu Uku, Muhammad Show Man, Fati Washa, Umma Shehu, Fati Shu’uma, Wasila Isma’il da Hadiza Maikano.
Jama’a ciki da wajen Kannywood sun kaɗu da wannan mutuwa.
Tun daga lokacin da aka ba da sanarwar rasuwar a daren jiya ko’ina ya ɗauka, duk inda ka leƙa soshiyal midiya maganar ake yi.
Wasu da dama sun yi haɗu da shi a ofishin sa, wasu kuma a wurin da Allah ya ɗauki ran sa.
A saƙon ta’aziyya da ya aika wa iyalan mamacin, ɗan Majalisa mai wakiltar Mazaɓar Igabi ta Yamma a Majalisar Dokoki Jihar Kaduna, Honorabul Yusuf I. Zailani, wanda makusancin marigayin ne, ya ce: “Ina mai miƙa ta’aziyya ta musamman ga dangin marigayi El-Mu’az Birniwa, abokan sa, da dukkan al’ummar da suka yi rashin wannan bawan Allah mai daraja.
“Hakika wannan rashi babban jarrabawa ce gare mu, kuma muna roƙon Allah (SWT) Ya ba mu haƙuri da juriyar jure wannan babban rashi.
“Marigayin mutum ne mai nagarta, mai ƙaunar mutane, wanda ya kasance abin alfahari ga al’umma.
“Mun yi babban rashi, amma muna da tabbaci cewa Allah mai rahama zai gafarta masa kurakuransa, Ya sanya kabarin sa ya zama lambun Aljanna, kuma Ya ba shi makoma mai kyau a gidan lahira.
“Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya ƙarfafa zukatan iyalan sa da dangin sa, Ya ba su ikon jure wannan babban rashin.
“Kuma ina kira ga al’umma mu ci gaba da yi masa addu’a, domin addu’ar da ake yi wa mamaci ita ce mafi kyautar da za mu iya ba shi.
“Allah Ya jiƙan marigayi El-Mu’az, Ya gafarta masa zunuban sa, Ya kuma albarkaci zuriyar sa da tsira daga dukkan fitintinu.”

