GIDAN yanar nan mai watsa wa ‘yan kallo finafinan Hausa ta hanyar intanet, wato Kallo.ng, ya samu kyautar karramawa ta duniya, watanni takwas kacal bayan an ƙaddamar da shi.
Ya samu kyautar sabon gidan yanar watsa shirye-shirye da fi kowanne iya ƙirƙira, wato ‘Best New Streaming Innovation’, daga kamfanin Marketing World Awards (MWA), a taron shekara-shekara na 11 da ya gudanar a Ankara, babban birnin ƙasar Ghana, a ranar 15 ga Yuli, 2022.
Manajar Darakta kuma mamallakiyar kamfanin gidan yanar, Hajiya Maijidda Modibbo, ta bayyana farin cikin ta kan wannan karramawar wadda ta kira da “babbar nasara.”
A sanarwar da ta bayar a ranar Asabar, Maijidda ta ce ta samu wannan karramawar ne sakamakon aiki tuƙuru da ta ke yi da kuma hazaƙar ƙirƙira wadda ta sa ingancin gidan yanar ya yi daidai da yadda ake buƙatar sa a ko’ina a duniya.
A cewar ta, Kallo.ng ya yi nisa wajen amfani da dabarun fasaha na zamani domin ya zama mai tasiri kuma mai jan hankali, ba domin komai ba sai saboda ya biya wa masu son kallon finafinan Hausa buƙata.
Ta bayyana cewa a cikin watanni takwas da ya yi, gidan yanar kallo.ng ya samu sama da mutum 35,000 da su ka yi rajista su na amfani da shi, sannan yawan su zai ƙaru nan ba da daɗewa ba saboda ana samun ƙarin masu kallo da ke kallon finafinai ta hanyar gidan yanar.
Maijidda ta ce: “Wannan karramawa tukwici ne na aiki tuƙuru da mu ke yi domin biya wa abokan cinikayyar mu buƙata. Ƙungiyar da ta ba mu karramawar ƙungiya ce da aka san da ita kuma ake girmama ta a duniya.
“Karramawar, wadda mu ka samu bayan watanni shida kacal da ƙaddamar da gidan yanar, ba za ta sa mu shagala ba, a maimakon hakan sai ma ta ƙara mana ƙarfin hali domin mu biya wa abokan hulɗar mu buƙata kuma mu tafi daidai da ƙasashen da su ka ci gaba.”
Shugabar ta kuma faɗa wa waɗanda su ka yi rajista da gidan yanar da duk wani mai son finafinan Hausa cewa su sa ido su ga ƙarin abubuwan burgewa da cigaban da za ta kawo, waɗanda manufar su ita ce a ƙara inganta gidan yanar don ya tafi daidai da na ƙasashen da su ka ci gaba.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa kamfanin Spacekraft Media Limited ne ya kafa Kallo.ng a cikin watan Nuwamba, 2021.