• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, June 7, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Dattijo ya sha alwashin rungumar ‘yan Kannywood na Kaduna idan ya zama sanata

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 17, 2022
in Labarai
0
Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), a tsakiya; a kusa da shi (daga dama) El-Mu'az Birniwa, daga (hagu), Alh. Ahmad Maiyaƙi, Baban Kausar da sauran 'yan fim a yayin ziyarar

Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), a tsakiya; a kusa da shi (daga dama) El-Mu'az Birniwa, daga (hagu), Alh. Ahmad Maiyaƙi, Baban Kausar da sauran 'yan fim a yayin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar zama sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya (Kaduna Central) a jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Alhaji Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), ya amince ‘yan fim da mawaƙa su rubuto masa abubuwan da su ke so domin ya ga rawar da zai taka masu idan ya samu nasara.

Dattijo, wanda shi ne tsohon shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnatin Jihar Kaduna (Chief of Staff) kuma tsohon kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar (Ministry for Budget and Planning), ya bayyana haka ne lokacin da wasu gungun ‘yan fim da mawaƙa, a ƙarƙashin jagorancin kamfanin Birniwa Concept na fitaccen mawaƙi El-Mu’az Muhammad Birniwa da kuma wakilcin ƙungiyar 13×13 Movement ta ƙasa su ka kai masa ziyara a yammacin shekaranjiya Alhamis domin nuna mubaya’ar su a gare shi tare da bayyana goyon bayan su ga takarar sa. 

‘Yan Kannywood ɗin sun kai ziyarar ne domin tabbatar masa da cewar su na tare da shi a tafiyar siyasar sa kuma su na da ƙudirin tallata shi domin ganin ya kai gaci a zaɓen.

Baban Kausar tare da Dattijo

A yayin ziyarar, sun tattauna kan muhimman abubuwa na cigaba, waɗanda su ka shafi masana’antar baki ɗaya, musamman a kan rashin cigaban da ake samu da kuma rashin wasu abubuwa da za su sa masana’antar ta kai matsayin yadda takwarorin ta su ke a duniya, ba kawai a kan Kaduna ta Tsakiya da zai wakilta ba.

Haka kuma sun nuna za su ba shi gudunmawar su, shi kuma in Allah ya kai shi wannan wuri a matsayin sa na sanata ya gabatar da ƙudirorin su. 

Bugu da ƙari, sun tabbatar masa da cewa za su rubuta ƙudirorin su a rubuce.

Sannan sun yi magana a kan abin da ya faru a lokacin da ɗan Majalisar Wakilai Alhaji Abdulmumini Jibril Kofa ya yi yunƙurin ganin Gwamnatin Tarayya ta samar da ‘Film Village’ a Kano, kuma ƙudirin ya karɓu a majalisa, amma jama’ar Kano su ka ƙi.

Da ya ke mayar da jawabi a gare su, Dattijo ya nuna farin ciki kan goyon bayan su da ya samu, sannan ya amince da su rubuto ƙudirorin su ya duba, ya tantance, ya ga waɗanda su ka shafe da zai iya, ya sa hannu, su ma su sa hannu, sai ya zama sun shiga yarjejeniya tsakanin su da shi. 

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a yanzu dai ‘yan Kannywood ɗin za su zuba hannun jarin su ne na taya shi kamfen, domin ya kai ga samun wannan kujera don su ma su samu biyan buƙatun su a gwamnatance.

Tawagar ‘yan fim ɗin sun haɗa da El-Mu’az, Baban Kausar, Maryam Aliyu Obaje (Madam Korede), Sakina Mando, Ɗanbashari Birniwa, Babangida Birniwa da sauran su.

Loading

Tags: 13x13 MovementAbdulmumini Jibril KofaAPCBirniwa ConceptDattijoEl-Mu'az Muhammad Birniwa.film villageKaduna ta TsakiyaKannywoodKanoMajalisar WakilaimawaƙiMuhammad Sani AbdullahisanataZaɓen 2023
Previous Post

Ban tsaya yawon maula ba bayan na bar ‘Ɗaɗin Kowa’, cewar Sallau

Next Post

Abin da ya sa na kai wasu matasa kotu aka kulle su saboda ‘ya ta Iman – Mansurah Isah

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Mansurah Isah da Khadijatul Iman

Abin da ya sa na kai wasu matasa kotu aka kulle su saboda 'ya ta Iman - Mansurah Isah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!