MAWAƘIN da ya rera fitacciyar waƙar nan ta ‘Sambisa’, Malam Sani Liya-Liya, ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba zai fito sarari duniya ta san shi.
Shi dai Sani, shi ne wanda ya rubuta kuna ya rera waƙar ‘Sambisa’, to ba shi ne ya hau waƙar a faifan bidiyon ta ba, wani jarumi ne daban tare da jaruma Zainab Sambisa.
A tattaunawar sa da mujallar Fim, mawaƙin ya ce: “To gaskiya ni a lokacin da na yi waƙar ‘Sambisa’, na yi ta ne kawai na sake ta ba a bidiyo ba. To ita wannan yarinyar Zainab ita ce ta sayi waƙar a waje na ta yi bidiyo ita da Yamu Baba. To, sai ake ɗauka su ne su ka yi.
“Amma ni na rubuta waƙar na rera ta, su kuma su ka hau. Amma dai ina nan na shirya ‘Sambisa’ ta nan gaba; ni zan yi bidiyo da kai na, za a ga fuska ta, zan fito a matsayin wanda ya rubuta waƙar kuma ya rera ta.

“Don haka, mutane su jira nan gaba kaɗan za su gan ni a matsayin mawaƙin ‘Sambisa’ da na rubuta waƙar tun asali kuma na rera ta.
“Kuma zan yi wasu sababbin waƙoƙin da za su fito tare da ita.”
Da mu ka tambaye shi ko matsala su ka samu da ita Zainab Sambisa, wadda ta sa waƙar ta dawo wajen sa ya daina sayar mata, sai ya amsa da cewa, “Idan ma da matsala a baya, a yanzu mun daidaita. Don haka zan riƙa fitar da waƙar ne da kai na. Da man tawa ce na sayar masu”.
A kan yadda ya fara waƙa, Sani ya ce sha’awar finafinan Hausa ce silar sa ta shiga harkar waƙa, duk da kasancewar sa almajiri wanda ya yi yawon neman karatun Alƙur’ani.
Ya ce: “Asalin waƙa ta dai na fara ta ne a sakamakon kallon finafinan Hausa da na ke yi. Kuma sai na ga duk fim ɗin da na kalla to waƙar cikin sa ta na burge ni.
“To, daga nan kawai sai Allah ya cusa mani sha’awar harkar, kuma sai na fara kamar wasa. Ina gwadawa kamar wasa sai ga shi Allah ya taimake ni na zama mawaƙin da duniya ta fara sani na a matsayin mawaƙi.”
Dangane da irin waƙoƙin da ya ke yi, Liya-Liya ya ce, “Na yi waƙoƙin faɗakarwa da na yabon Manzon Allah (s.a.w.), sannan na yi waƙoƙin siyasa su ma da yawa, sannan na yi waƙoƙin bikin aure da ake kawo mani ina yi. Don haka zan iya cewa na yi waƙoƙi masu yawa a ɓangarori da dama na rayuwar jama’a.”
Sani Liya-Liya ya yi fatan alheri ga dukkan masoyan sa, tare da bayyana fatan Allah ya bar su tare.
![]()







