A RANAR Juma’a, 28 ga Oktoba, 2022 Allah ya azurta mawaƙi Sulaiman A. Tijjani, wanda aka fi sani da Farfesan Waƙa, da matar sa Sadiya Adamu (Mama Queen) da santaleliyar ‘ya mace.
Sadiya ta haihu da misalin ƙarfe 12:00 na dare a gidan Farfesa da ke unguwar Darmanawa, Kano.
Da ranar ta zagayo, wato ranar Juma’a, 4 ga Nuwamba, aka raɗa wa jaririyar suna Maryam, amma su na kiran ta da Princess Mama.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa da yake sunan mahaifiyar sa ne Farfesa ya raɗa wa ‘yar sa, sai su ke kiran ta da Princess Mama, kamar yadda ake kiran mahaifiyar ta Mama Queen.
An yi taron raɗin sunan ne a gidan iyayen Farfesa da ke garin Faki, Jihar Kaduna, bisa al’ada.
An kuma yi taron shagalin bikin sunan a gidan sa da ke Darmanawa, Kano.
Farfesa ya yi wa Allah godiya da samun wannan arziƙi na ‘ya da ya yi.
Ya faɗa wa mujallar Fim: “Babu abin da zan ce sai godiya ga Allah domin wannan babban arziƙi ne ya ba ni. Shi arziƙi ba lallai sai na kuɗi ko wani abu ba.
“Don haka ina cikin farin ciki maras misaltuwa. Allah ya raya mana ita, ya kuma albarkaci rayuwar ta.”
Shi dai Farfesan Waƙa, an ɗaura auren sa da Sadiya ne a ranar Laraba, 15 ga Disamba, 2021 a ƙofar gidan Alhaji Sa’adu Komados da ke Titin Faska, Tudun Wadan Ɗankadai, Jihar Kano.
Allah ya raya Maryam (Princess Mama), amin.