A WANNAN rana ta Juma’a, 10 ga Fabrairu, 2010 aka ɗaura auren jaruma Khadija Alhaji Shehu Yobe, wato Karima a cikin ‘Izzar So’, da mawaƙi Izzuddeen M. Doko.
An ɗaura auren a Masallacin Juma’a na unguwar Nassarawa da ke garin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, da misalin ƙarfe 2 na rana.

Tun a ranar Alhamis an yi taron shagalin biki a Damaturu, wanda ‘yan fim da dama su ka halarta domin taya ango da amarya murnar bikin nasu.
Asma’u Sani, ɗaya daga cikin ‘yan fim da su ka halarci bikin, ta shaida wa mujallar Fim cewa an yi bikin an ƙare lafiya.
Da fatan Allah ya ba da zaman lafiya.






