MAWAƘIYA a Kannywood, Maryam A. Baba (Sangandale), ta yi addu’ar cewa Allah ya zaunar da ita a gidan mijin ta har zuwa ƙarshen rayuwar ta.
Maryam ta faɗi haka ne a daidai lokacin da auren ta da mawaƙi Abdul Kafino ya cika shekara uku.
Ma’auratan sun yi wani hoto na musamman domin nuna godiya ga Allah da ya nuna masu wannan lokacin.

A cikin wani saƙo da ta wallafa a Facebook mai nuna ta bayar da amsa ne ga wata tambaya da wani ya aika mata, shararriyar mawaƙiyar ta ce, “Wani ya ce wai Allah ya sa ni ma ba kashe aure na na yi ba. Na ce masa amin.
“Hmmmm… abin da ba ka sani ba komai muƙaddari ne daga Allah, kuma bawa ba ya kauce wa ƙaddarar sa. Amma aure na in-sha Allah mutu-ka-raba. Har Aljanna ina sa ran mu na tare da miji na bi’iznillah.”
