• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

YADDA FATI NIJAR TA BAJE KOLIN TA A BIKIN ZAHRA BUHARI

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 7, 2017
in Labarai
0
YADDA FATI NIJAR TA BAJE KOLIN TA A BIKIN ZAHRA BUHARI
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Bikin auren diyar Shugaban Kasa, Zahra Buhari, da mijin ta Ahmed Indimi da ya gudana a cikin watan jiya biki ne da ya dauki hankalin mutane a ciki da wajen kasar nan. Ya kasance abin tattaunawa a duk wajen taruwar jama’a da ma wadanda su ke kan hanya su na tafiya. 

Kamar yadda bikin ya ja hankalin mutane, haka ma zuwan fitacciyar mawakiya Fati Nijar ya dauki hankalin mutane domin ita kadai ce mace da ta halarci bikin a duk mawakan Kannywood. Wannan ya kara fito da matsayi da kuma shaharar da Fati ta ke da shi a cikin abokan sana’ar ta.

Baya ga haka, ko a wajen bikin da aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja, Fati Nijar ta zama kallabi tsakanin rawuna, domin kuwa akwai mawaka maza da dama na Kannywood da su ka halarci bikin, amma duk ba a san da zuwan su ba. Yawancin su sun tashi a matsayin ’yan kallo ne, don kuwa har su ka je su ka dawo ba a san da zuwan su ba; duk da yadda aka yada hotunan bikin a duniya, sam ba a nuno hotunan su ba. Hotunan Fati kadai aka yada a duniya ta na zuba waka.

Fati Nijar (Gimbiyar Mawakan Borgu) ta shaida wa wakilin mu cewa ta halarci bikin ne don ta yi waka a ranar Kamun Amarya, amma sai abin ya zame mata biyu, don kafin a yi kamun sai Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari, ta shirya wani zama na musamman wanda ba kowace mace za ta halarci wajen ba sai matan gwamnoni da ministoci da wasu kasaitattun matan kadai, to kuma sai aka kira Fati don ta zama zabiyar wajen daga ita sai manyan baki, aka ba ta lokaci ta yi sharafin ta, aka sha rawa ba irin ta gala ba.

A ranar Kamu ma dai Fatin ce ta yi zarra a cikin mawaka, saboda ko a nan ma ita ta ce dauke hankalin mahalarta bikin cikin wakokin ta masu kayatarwa, don haka ba abin mamaki ba ne da mutane su ke cewa idan ban da amarya da ango, to babu wani mutum da ya dauki hankalin mutane kamar Fati Nijar.

Da mu ka tambaye ta yadda ta ji a wajen wannan biki, cewa ta yi, “A gaskiya wannan abin ina alfahari da shi kuma ina kara yi wa Allah godiya. Domin kuwa abin alfahari ne a gare ni kasancewa ta a wajen wannan biki. Duk da na sha halartar wajen bukukuwa da yawa ina yin waka, amma dai ba kamar wannan ba. A ce an gayyace ka bikin ’yar Shugaban Kasa, ka je ka zama mai waka a wajen ai ka ga abin alfahari ne. Ni na san ba iyawa ta ba ce, daukaka ce daga Allah, kuma ina kara godiya a gare Shi bisa ni’imar ya yi mini. Ina rokon Sa kuma Ya kara mini basira da godiya a gare Shi.”

Daga karshe, Fati Nijar ta yi fatan Allah Ya kara hada kan mawaka, Ya daukaka sana’ar su.

To, amin.

Loading

Previous Post

AN BAI WA MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI’AR NOUN SARAUTA A INUGU

Next Post

CEWAR ADAM A. ZANGO: YANZU NA DAINA RIGIMA DA KOWA

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Adam Zango

CEWAR ADAM A. ZANGO: YANZU NA DAINA RIGIMA DA KOWA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!