FITACCEN manazarcin harkar adabi din nan, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya samu sarautar Nze Okaa Omee na Masarautar Ezema Olo da ke cikin Karamar Hukumar Ezeagu a Jihar Inugu.
Sarkin garin, Eze Ogbunechendo, Lawrence O.C. Agubuzu, shi ne ya nada shi sarautar a lokacin da ya ke bikin cikar sa shekara 10 kan gadon sarauta.
An yi bikin a ran Asabar, 17 ga Disamba, 2016 a kauyen Awene da ke cikin masarautar.
Farfesa Abdalla, wanda yanzu shi ne Vice-chancellor, wato Mataimakin Shugaban jami’ar nan ta tafi-da-gidan-ka, wato National Open University of Nigeria (NOUN), ya yi fice a fagen nazarin harkar finafinan Hausa, rubutun kirkira da kuma kade-kade kusan ma fiye da kowane malamin jami’a a kasar nan.
An yi masa wannan nadi ne saboda yadda ya ke kawo sauye-sauye masu alfanu domin ciyar da jami’ar gaba.
Shi basaraken da ya yi nadin shi ne Shugaba (Chancellor) na jami’ar), kuma wannan nadi ya na nuni ne da gamsuwar sa da yadda malamin ke gudanar da mulkin jami’ar.
Sarkin na Ezema Olo, wanda tsohon Jakaden Nijeriya ne a kasashen Zambiya da Malawi, shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Inugu.
A sanarwar da daraktan yada labarai na jami’ar ta NOUN, Malam Ibrahim Sheme, ya raba wa ‘yan jarida, an bayyana cewa a jawabin nada Farfesa Abdalla da Igwe Agubuzu din ya yi, ya ce malamin ya cancanci wannan nadi ne saboda gagarimin canji mai alfanu da ya ke kawowa tun bayan hawan sa shugabancin jami’ar a kasa da shekara daya kacal.
Ya ce farfesan ya kawo tsarin keke-da-keke tare da bin ka’idojin aiki, kuma duk abin da ya sa a gaba sai ya kai ga nasara.
Har ila yau, basaraken ya roki Mataimakin Shugaban Jami’ar da ya kasance ya na saka jar darar sa da ya dora masa a ko’ina ya ke a cikin kasar nan don alamta cewa shi ma ya na daya daga cikin masu sarauta a yankin.
A nasa jawabin, Farfesa Abdalla ya bayyana farin cikin sa da wannan nadi da aka yi masa, kuma ya yi alkawarin zai kara zage damtse wajen habaka ilmi a kasar nan.
Daga nan sai ya tashi ya dan taka rawa tare da bin sarakin yankin ya na yi masu godiya a gaban dubban ‘yan kallon da su ka halarci kasaitaccen bikin, kamar yadda al’adar garin ta ke.
Wannan ne karo na farko da aka taba bai wa Farfesa Abdalla sarautar gargajiya, inda bayan bikin ya shaida wa tawagar da ta take masa baya daga jami’ar cewa ya na matukar alfahari da wannan nadi da aka yi masa.
Tsohon shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwa ta jami’ar NOUN, Sanata Abeh Ebute, shi ne ya jagoranci tawagar jami’ar zuwa bikin, yayin da Mataimakiyar Gwamnan Enugu, Mrs. Cecilia Ezeilo, ta wakilci gwamnan jihar. Manyan sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ‘yan siyasa da sauran dimbin jama’a daga cikin jihar da sauran sassan kasar nan sun halarci bikin.
![]()








I have been surfing online more than 3 hours today, yet
I never found any interesting article like
yours. It is pretty worth enough for me. Personally, if all webmasters
and bloggers made good content as you did, the internet will
be a lot more useful than ever before.