• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rawa, Waka Da Gurbatattun Finafinai

by DAGA ASHAFA MURNAI BARKIYA
January 6, 2017
in Tsokaci
0
Adam A. Zango da Fati Washa su na rawa a wani fim

Adam A. Zango da Fati Washa su na rawa a wani fim

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAN yi mamaki ba da na ga a cikin Fim ta watan Oktoba 2016 Malam Ahmad Alkanawy ya fito ya ce yawancin finafinan Hausa gurbatattu ne. Wannan jama’u da ya yi kuwa ya hada ne da ‘yan fim gaba daya. Duk da dai har yau ban samu damar karanta abin da ya rubuta ba, amma an fi shekara goma na sha so na yi magana a kan yadda ake shirya wasu finafinai ana sakar wa al’umma su na kallo. Maganar da furodusa kuma darakta Alkanawy ya yi ce ta sa na ce ya kamata ni ma a yanzu na dan ce wani abu.

Tun farko na san an fara sukar rawa da waka ne a finafinan Hausa. Duk da cewa dai harkar rawa da waka a finafinan Hausa duk al’adar Indiyanci ne fafur aka wanko, ban maida kai wajen kushe su ba a wancan lokacin, saboda na dauke su a matsayin nishadantarwa.

Inda na fara daka wa wakokin fim harara shi ne tun a wani fim mai suna ‘Wankan Gida’, wanda Ali Nuhu ne jarumin fim din, shi da marigayi Musa Jalingo. Kuma fim din na Musa Jalingo ne. Bari na bada labarin fim din yadda mai karatu zai fahimci inda tantagaryar barnar ta ke.

Ali da Musa sun fito ne a matsayin ma’aikata wadanda ofishin su daya. Abokai ne, kuma dukkan su manema mata. Sai Ali ya tura matar sa gida ta yi wankan jego. Hakan ya bude masa kofar neman mata fafur. Bayan tafiya ta yi nisa sai ya rika yin karyar zai tafi taron semina a wani gari, amma sai ya je wani wuri ya kwanta ya rakkashe.
To wata rana ya yi mata karyar cewa ya yi tafiya, ya aka yi sai ta je ofis din. Da yake na kai shekara goma da kallon fim din, na dan manta wasu sinasinan da ke ciki. Shi kuma Musa ya san Ali ba wani taro ofishin su ya tura shi don ya halarta ba.

Da matar Ali ta shiga ofishin, sai Musa ya tambaye ta lafiya kwana biyu bai gan shi ofis ba? Sai ta yi mamaki, ta ce, “To ni dai ce min ya yi ya tafi taro kuma daga nan ofis aka tura shi.” Shi fa Musa ya san komai, amma sai ya yi mamaki ya ce, “Gaskiya ba haka ba ne.” Ya aka yi bai sani ba? Ya yi haka ne saboda hankalin sa ya tashi ya na so ya neme ta. Da ma a fim din shi da Ali duk kwaryar sama ce ke dukan ta kasa.

Daga nan kawai sai aka nuno Musa na yi wa matar nan kallo irin na manema mata. Ga ta fa a cikin hijabi. Da aka gwalo fuskar Musa ya kura mata idanu, daga nan kawai abin ka da fim din Hausa, sai aka nuno shi da matar su na rawa da waka a cikin fulawa. Ga ta kuma sanye da hijabi. Inda aka kara yin nitso a cikin lalata fim din shi ne irin wakar da su ke yi. Shi dai da kwartanci ya ke son ta. Sai ga shi tare da matar abokin sa ta na sanye da hijabi su na waka mai taken:  “Yabon Manzon Allah, akwai tsantsar dadi.” Abin takaici fa wai tunani shi Musa din ya ke yi a fim din.

Bayan na kalli fim din sai na kira Musa Jalingo. Mu ka yi mahada da shi a Zoo Road, Kano. Na ce masa, “Na kalli ‘Wankan Gida.’ Tambayar da zan yi maka, shin al’adar wadanne Hausawa ne ke rawa a cikin fulawa tare da matar wani? Hausawan Katsina ko na Jos ko na Bauchi ko Sakkwato? Me ya kai kwarto da matar wani a cikin fulawa su na yabon Manzon Allah?”

Sai da ya bari na gama kumfar baki, sai ya yi dariya ya ce, ‘‘Ashafa kenan! Ka je ka yi jaridancin ka, mu ka bar mu mu nemi kudi kawai.”

Ban da wannan fim din, akwai kuma wani wanda na manta sunan sa, amma Samira Ahmed ce jarumar sa tare da tsohon mijin ta, T.Y. Shaban, da kuma Bashir Kaya a matsayin abokin jarumi. Shaba da Samira duk a karkara aka haife su. Aka daura wa Shaba aure da Samira. Amma abin ka na sakarcin Bagidaje maras ilmi (kamar yadda aka nuna a fim din), daga wasa sai ya yi mata saki uku.

Haka ya hakura da ita, ta yi aure a birni, ta auri Bashir Kaya. A takaice, Shaba ya shigo birni neman aiki, kuma Bashir ya dauke shi aiki rashin sani. Ganin da ya yi wa Samira a gidan ya tayar masa da hankali. Ita kuma da ma tun da ta gan shi sai ta rika boyewa, ba ta son ganin sa. Ta damu mijin ta ya ba shi jari kawai ya sallame shi. Bayan an sallami Shaba, an ba shi jari, shi ma ya faso gari, sai kuma ya koma shi ko ta halin kaka sai Samira ta dawo masa. A irin haka ya na cikin tunani shi ma sai aka nuno shi ya na rawa da waka tare da Samira, matar Bashir.

Zan yi tambaya, tunda an ce fim din Hausa ne ake shiryawa: don Allah Hausawan ina ne ke shirya mana irin wadannan finafinan? Anya Hausawan Barkiya ko Gusau ko Daura ko na unguwar Yakasai ne a cikin Kano? Daga ina irin wadannan Hausawan su ka fito ne? Hausawan ne kuwa? Ko dai ‘mun ji Hausa’ ne?
Babbar matsala kuma a cikin finafinan mu, da yawa yara matasa ne wadanda hankali bai game musu jiki ba, su ne ke rubuta labaran. Ba su san muhimmancin tarbiyya ba, ba su mallaki iyali ba. Iya zurfin tunanin su ya ci burki ne a kofar gidan soyayya kawai. A wurin su, soyayya ita ce komai, shi ya sa sai su gina kowane labari a kan namiji da mace, saurayi da budurwa ko kuma a kan abin da namiji ke kwadayin neman biyan bukata daga wajen mace.

Ina daga cikin masu ra’ayin cewa ba dole sai an yi rawa da waka sannan fim zai karbu ba. Ban kuma ce a daina yin rawa da waka ba, amma yawancin wadanda ake yi ba su ma da dalili ballantana tasirin yin su a cikin fim din. Ana fara fim wani ma kafin minti biyar da farawa sai ka ga an kacame rawa da waka, kuma wakokin da ba su da matsuguni, gidan haya ko gidan kan su a cikin al’adar Bahaushe.

An wayi gari ko Bahaushe bai taba zuwa Indiya ba, da ya kalli wasu finafinan Hausa zai fahimci irin yadda rayuwar Indiyawa ta ke. Daraktoci, furodusoshi da masu rubuta labaran finafinai har yau sun takaita tunanin su wuri daya, an kasa matsawa gaba. Tuni aka saki al’adar Hausawa da Fulani aka shigo mana da Bayarabiyar al’ada ko Ba’Indiya da sauran kananan al’adun da ke Gabas da Kano, irin su Baburanci, Jukunanci, Tangalanci da sauran al’adun da sun ci karo da na Bahaushe muraran.

Babu ruwan yawancin furodusoshi da tarbiyyar ‘ya’yan mai kallon finafinan su. Su dai idan aljihu ya cika, to gidan kowa ma ya lalace. Yanzu ta kai akwai finafinan Hausa da yawa wadanda har ma gara ka sai wasu fim din Indiya ka kai gida da ka bari a kalli wadannan finafinan a gidan ka.

Su kuwa  yawancin ‘yan fim mata da ma babu ruwan su, duk abin da aka ce ki yi, in dai zai kai ki ga yin fice da shahara, shikenan, kin samu hanyar kama kantamemen gida ko sayen kantamemen gida da motar  na-faso-gari. Wasu da ma iska ne ya iske kaba na rawa. Amma fa duk da sunan masu shirya finafinan Hausa!

An wayi gari a yau ana shigo da sakarci samfur-samfur da sunan finafinan barkwanci. Duk abin da yaro bai sani ba, idan ya kalli fim din Hausa zai sani, ko da a gidan su ana boye masa. A da can daki kawai za a nuno an nufa, yanzu kuma har kokowa da wasanni a kan gado za a nuno. Ta kai ma har rigar nono da siket da dan kamfai ake nunowa an jefar a gefen gado. Shin dole ne sai mun kwaikwayi finafinan Amurka? Duk da fitsarar Amurka su na daukar matakai kan yawan shekarun da yaro zai kai kafin ya kalli wasu finafinan. Amma mu kuwa Hausawa mu ma mun biye wa ‘yan fim  din, duk fim din da mu ka ga Halima Atete ko Rahama Sadau ko Sadiq Sani Sadiq ko Ali Nuhu ko Bosho ko Hadiza Gabon, sai mu kwasa mu kai gida, wai mu ga gwanayen mu. Ba ka ma tsayawa ka tantance abin da fim din ya kunsa.

Lokacin da na je Kano hutun Babbar Sallah, na kalli tallar wani fim mai suna ‘Tsakar Gidan Jatau.’ Idan haka fim din zai fito kamar yadda na kalli tallar sa, ba na fata wani yaro ko yarinya ta kawo shi a tsakar gida na a kalla. Ko fim din ya fito yanzu ya game duniyar Hausawa? Ni dai ban sani ba.

Loading

Tags: Finafinai
Previous Post

’YAR FIM

Next Post

AN BAI WA MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI’AR NOUN SARAUTA A INUGU

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Farfesa Abdalla Uba Adamu

AN BAI WA MATAIMAKIN SHUGABAN JAMI’AR NOUN SARAUTA A INUGU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!