SUNAN FIM: ’Yar Fim
KAMFANI: Maikwai Movies
LABARI: Abubakar A.S. Maikwai
TSARA LABARI: Yakubu Kumo
DAUKAR NAUYI: Usman A.S. Maikwai
UMARNI: Abubakar A.S. Maikwai
JARUMAI: Ali Nuhu, Nura Hussain, Sadiq Sani Sadiq, Jamila Umar Nagudu, Ladidi Fagge, Hajara Usman, Halima Atete, Hafsat Idris.
FIM din ya na bayar da labarin wata shahararriyar jarumar fim ce mai suna Fati Muhammad (Hafsat Idris) wacce ta kasance mai saukin kai da mu’amala mai kyau. A haka ta hadu da wani masoyin finafinai, Hadi (Sadiq Sani Sadiq), shakuwa da soyayya mai karfi su ka shiga tsakanin su har su ka amince wa juna za su yi aure. Sai dai a bangaren Hadi mahaifiyar sa, Hajiya (Hajara Usman), da matar sa Yasira (Jamila Nagudu), sun ki yarda da auren, amma da yake ya sami goyon baya daga gurin mahaifin sa sai da aka yi auren.
Ranar da Fati ta tare gidan Hadi yayan Yasira (Nura Hussain) ya zo ya tafi da ita, ya ce kanwar sa ba za ta zauna da ’yar fim ba. Duk yadda Hadi ya so hana tafiyar amma sai da su ka tafi.
Fati ta ci gaba da kyautata wa mijin ta da dangin sa har ta samu ta shawo kan uwar mijin ta, daga karshe ma da kan ta ta je bikon Yasira ta dawo da ita dakin mijin ta.
ABUBUWAN BURGEWA
Fim din ya isar da sakon da ake son ya isar, domin ya yi kokarin nuna yadda ake yi wa ’yan fim kallon banza daga nesa, amma idan su ka matso kusa sai a ga sabanin hakan. Sannan jaruman fim din sun yi kokarin isar da sakon da fim din ke tafe da shi.
KURAKURAI
1. An yi kokarin nuna Fati mai tarbiyya ce kuma daga gidan su ta ke fitowa ta tafi gurin fim. Ya kamata a ce an nuna wa mai kallon hakan, da rayuwar ta a gidan iyayen ta, domin hakan ne zai gamsar da mai kallo wacece ita.
2. Yadda aka nuna Fati ta na da tarbiyya, ya kamata a ce ta na saka gyale, maimakon yadda ta ke yawo haka a gari.
3. Tun da aka fara fim din har aka gama ba a san sana’ar Hadi ba. An dai ga gidan sa mai kyau da kuma babbar motar da ya ke hawa.
4. An ce Yasira kazama ce, amma kuma yanayin shigar ta bai nuna hakan ba, kullum za a gan ta fes-fes cikin kwalliya.
5. Tunda an nuna Hadi mai tarbiyya ne, to bai kamata ya dinga sa-in-sa da mahaifiyar sa ba.
6. Bayan Hadi ya auri Fati, sai ya zamto a dakin barci Yasira ita ma ta ke zaune.
7. Yadda aka nuna iyayen Hadi dattawa ne, musamman mahaifin sa, ya kamata su yi magana ko sau daya ne a kan tafiyar Yasira daga gidan sa.
8. Irin aikin da aka nuna Fati ta yi na gyaran gida da girki da karatu da ta koyar da mai aiki girki da sauran abubuwa sun yi yawa a ce an yi su a yini guda kacal.
9. Yadda aka nuna Hadi, mai kallo ya kasa gane waye shi, domin akwai kwan-gaba-kwan-baya a kan halayyar sa, domin shigar sa da yanayin sa sun fi kama da niga amma mu’amalar sa wani lokacin ta yi ta kamar nija, wani lokaci mai bada dariya, da sauran su.