• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Karatun Jami’a: Sai fa mun tashi tsaye!

by DAGA FARFESA ABDALLA UBA ADAMU.
March 28, 2018
in Tsokaci
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Jama’a, assalamu alaikum.

MANUFAR Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (National Open University of Nigeria) ita ce samar da ingantaccen ilimi ga miliyoyin ’yan Nijeriya ta hanya mafi sauki, wato hanyar da mu ke kira Open and Distance Learning (ODL), wanda wasu ke fassarawa da “Karatu Daga Gida”. Shi wannan tsari, dimbin kasashe sun rungume shi saboda hangen nesan da aka yi cewar mutum zai iya yin karatu mai zurfi daga duk inda ya ke, ba lallai sai ya tafi aji ya zauna malami na karantar da shi ba. Yanzu ma abin ya kara saukaka saboda hanyoyin sadarwa na zamani da ake da su. Yanzu ga intanet nan, ta yadda ka na zaune a dakin ka ko shagon ka ko gonar ka sai ka yi karatun ka a tsanake – ta hanyar komfutar ka ko ma wayar hannun ka; ga kuma littattafai da za mu ba ka don ka yi amfani da su.

A Nijeriya, tun a shekarar 1983 (zamanin mulkin Shagari) Gwamnatin Tarayya ta kafa wannan jami’a don cimma wannan kudiri. An dakatar da jami’ar bayan shekara daya saboda wasu matsaloli, to amma a zamanin mulkin farar hula na Obasanjo sai aka farfado da ita. Yanzu ga ta nan ta bunkasa, ta yi yabanya. A yau, mu na da dalibai sama da 400,000 da su ka yi rajista.

Sai dai abin bakin ciki, kamar yadda na fada wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi lokacin da na ziyarce shi kwanan baya, mu a Arewa an bar mu a baya wajen rungumar wannan sassaukar hanya ta karatu a bisa tsarin ODL. Yawancin daliban mu ’yan Kudu ne. A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta buga a ranar 10 ga Mayu, 2017, sakamakon wani bincike da ta yi kan tsarin karatun mu, an gano cewar idan ka dauki jihohi guda bakwai na Kudu, wato Delta, Imo, Ogun, Edo, Anambra, Osun da Oyo, daliban su a NOUN sun kai mutum 186,023 daga cikin jimillar dalibai 399,260 da ke karatu a jami’ar a lokacin. Wato kenan su bakwai din nan su na da kashi 47 cikin dari na dukkan daliban da ke jami’ar.

Jihar Delta ta fi kowace jiha yawan dalibai a NOUN, domin kuwa ta na da dalibai 33,416 a lokacin; sai Ogun na da 30,635; Imo – 27,752; Edo – 26,060; Anambra – 25,850; Osun – 22,915 da kuma Oyo – 19,395.

Idan an kwatanta su da jihohin Arewa kamar guda shida, wato Sakkwato, Yobe, Zamfara, Kebbi, Jigawa da Gombe, su ne ke da mafi karancin daliban, wato mutum 6,389 kacal, wanda dududu bai wuce kashi 1.6 na jimillar daliban mu ba. 

Jihar Sakwato (mai dalibai 684) ita ce koma-bayan kowace jiha wajen yawan dalibai a NOUN a daidai watan Afrilu na wannan shekara ta 2017; daga ita sai Yobe mai dalibai 766; yayin da Zamfara ke da 793; Kebbi – 1,154; Jigawa – 1,218, sai Gombe – 1,774. Yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja, na da dalibai 1,344 a lokacin. Har yanzu kuwa alkalumna da ke nuna wannan tserayyar da aka yi wa Arewa ba su wani canza ba.

Mun san cewa da ma can an bar Arewa a baya a fagen ilimin zamani saboda yadda tarihin abin ya faro, to amma kuma fa akwai rashin sani, wanda aka ce ya fi dare duhu. A yau Arewa na da miliyoyin dalibai da ke son shiga jami’a. Wadansu, yara ne da su ka gama sakandare ko wata babbar kwaleji irin su FCE; wasu kuma ma’aikata ne da ke son zuwa karo karatu; wasu matan aure ne ko zawarawa, wasu kuma masu sana’o’i ne kamar ’yan kamasho ko direbobi. Sau da yawa, ba su iya barin aikin da ke gaban su don su tafi jami’a. Wasu kuma sun yi ta rubuta jarabawar JAMB, amma ba a dauke su a jami’a ba, su na ta fama a duk shekara. Lokaci kuma na wucewa.

Kwanan nan, Babban Sakataren Hukumar Jami’o’i ta Kasa (National Universities Commission, NUC), Farfesa Abubakar A. Rasheed, ya bada wata sanarwa inda ya ce a gaskiya jami’o’in kasar nan sun yi karanci ta yadda ba za su iya dauke dukkan daliban da ke son shiga jami’a ba. Ya ce kashi 30 cikin dari na daliban da ke takarar shiga jami’a kadai ne za a iya dauka, daga cikin sama da dalibai miliyan daya da dubu dari bakwai (1.7m) da ke neman shiga jami’a.
To, menene abin yi? Amsa ita ce: duk su zo NOUN! Shi ma Farfesa Rasheed haka ya ce. A cewar sa, NOUN ita ce ta ke da karfin zuke yawancin daliban da su ka kasa samun gurbin shiga jami’a ta hanyar jarabawar JAMB.

Saboda haka mu na kira ga ’yan Nijeriya, ba ’yan Arewa kadai ba, da su rungumi wannan sabuwar hanya ta yin karatu daga nesa. Hanya ce budaddiya, mai sauki, mai rahusa. Ba sai ka bar abin da ka ke yi ba. Idan aiki ka ke yi, ka ci gaba da aikin ka. Idan ke matar aure ce da ke kula da gida da yara, ki ci gaba da auren ki, kuma kin a karatun ki a dakin ki. Idan a tasha ka ke neman abin sakawa a bakin ka, ka ci gaba da sana’ar ka a yayin da ka ke nazarin ka. Abin da kawai mu ke so shi ne ya kasance ka samu credits guda biyar, ciki har da Lissafi da Turanci. Ba ruwan ka da jarabawar JAMB.

Za mu ci gaba da fadakar da mutane. Shi ya sa za mu ka shirya taro a Kano, tare da hadin gwiwar kungiyar masu shirya finafinai, wato MOPPAN, domin su kamar wani tsani ne tsakanin mu da matasa a Arewa. Kuma mun nada Jakadun NOUN daga cikin ’yan fim din, wadanda za su taimaka mana wajen yayata sunan wannan jami’a da manufofin ta. Haka kuma mu na shirya guntayen finafinai wadanda kowannen su bai fi minti hudu zuwa biyar ba, wanda mutum zai iya kallo ko da ya na karyawa ne kafin ya fita zuwa aiki, don kara yi wa mutane bayanin wannan jami’a.

Mu na fatan sauran jama’a za su taimaka wajen wannan yaki na wayar da kan ’yan’uwan mu game da wannan muhimmin tsari na karatu ta hanyar ODL – Open and Distance Learning. Kamar yadda na ce, an yi mana nisa, kuma ana ci gaba da yi mana nisa. Saboda haka tilas mu tashi tsaye mu dage wajen neman ilimi ta hanyoyi na zamani.

Allah Ya ba mu sa’a, amin.

Loading

Tags: Sai fa mun tashi tsaye!
Previous Post

Shekaru 19 da kafuwar mujallar Fim: Jajircewa ce ta kawo mu yau

Next Post

Kaddarar Mu

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Kaddarar-Mu

Kaddarar Mu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!