• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kaddarar Mu

by DAGA MUHAMMAD LAWAL PRP
March 28, 2018
in Marubuta
0
Kaddarar-Mu

Kaddarar-Mu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
LITTAFI:                 Kaddarar Mu (1-4)
MARUBUCIYA:     Sa’adatu Isah Muhammad 
KAMFANI:             Nazzy Bookshop, Kano 
SHEKARA:             2017 
SHAFUKA:             144 
FARASHI:             N200 
ISBN:                     Babu
 
SA’ADATU Isah Muhammad sabuwar matashiyar marubuciya ce a bangaren rubutun zube, kuma sananniyar mawakiya a masana’antar finafinan Hausa, inda aka fi sanin tad a suna Sa’a bocal. Sa’a ta fara rubutu a shekarar 2013 da littafin ‘Kauna Ce Sila’ amma bai fita ba sai a 2015. Daga nan sai ‘Kaddarar Mu’ da ya fita a 2017. 

Labari 
Labarin wasu ’yan mata ne guda uku: Fadila, Farida, da kuma Fauziyya, wadanda kawancen su ya kullu ta sanadin kaddarar da ta hada su. Suna da uwargijiya, Hajiya Baraka, wadda a gidan ta Fadila da Farida su ke zaune. 

Dukkan su sun yi alkawarin babu su babu soyayya da wani da namiji balle batun aure. A haka Allah Ya hada Fauziyya da Likita Ahmad inda su ka fara soyayya mai karfi a tsakanin su, wanda ya janyo su Fadila su ka fara yunkurin hallaka saurayin likitan. 

Jigo 
  – Littafin na nuna illar tara abin duniya ta mummunar hanyar kawalci, kamar yadda Hajiya Baraka ta yi, a karshe ta kare a wulakance. 

  –  Amfanin tuba ga mai zunubi. Kada mai sabo ya fidda rai daga samun rahamar Allah. Duba rayuwar Fauziyya a karshe. 

Salo 

Marubuciyar ta yi amfani da salo mai karsashi wajen isar da sakon ta. Duk da yake babu gwanintar harshe sosai, amma salon ya yi kyau, haka taurari da garuruwan labarin sun dace da yanayin sa. Sai sambarka. 

Zubi Da Tsari 

An zubo labarin ne ratata, ba tare da babi ko kanun labari ba. Tsarin labarin ya samu kulawa mai kyau, ta yadda yake rike mai karatu babu kosawa. 

Ka’idojin Rubutu 

An samu kurakurai wajen ka’idojin rubutu a littafin, musamman wajen saka alamomin rubutu ba a gurbin da su ka dace ba, da kuma wajen raba kalma da hade ta. 

Ya kamata a kula kafin dab’i. 

Kurakurai 

1. Ba a amfani da alamar motsin rai (!) fiye da daya ko da sau nawa aka maimaita kalma. Duba shafi na 5 littafi na 1, wurin kiran Idi. 
2. A bangon littafi na 1 da na 2 ba a lankwasa harafin ‘K’ ba, wanda (hakan) ya mayar da sunan littafin  ‘Kaddarar Mu.’ 

3. Da wanne makulli Baraka ta kulle kawar ta Ruky da mijin ta Jamilu a daki kafin ta yi yunkurin kona su? Ko dai shirin nasu ya kai ya ba ta makullan dakin sa a lokaci kadan? Duba shafi na 38, littafi na 1. 

4. Shafi na 39, littafi na 1: Hukuncin wata shida ya yi kadan ga Baraka, idan an yi la’akari tsarin dokar kasa, yunkurin kisan kai ya na debo wa mutum shekaru ne a gidan maza. 

5. A shafi na 51, littafi na 1 Hajiya ta jefa wa Kwamishina hoto ta na yi masa barazana. A ina ta samu hoton, bayan kwanan ta daya a sel? Ko kuwa da ma yawo ta ke da shi? 

6. Shafi na 118, littafi na 1: Fauziyya ta ce ba ta san makarantar da za a kai ta ba, amma sai ga shi ta ce daga jin sunan makarantar za a yi karatu. Da ma ana gane makaranta mai karatu daga suna? 

7. Shafi na 39, littafi na 2: Lokacin da Fadila ta fito daga bandakin otal an ce sanye ta ke da tawul, amma har ta ja ‘yan’uwan ta su ka gudu ba a nuna inda ta canza kaya ba. Ko dai daga ita sai tawul ta gudu? 

8. Shafi na 105, littafi na 2: An nuna Fadila ta fara shaye-shayen kayan maye kai-tsaye. Ya kamata a ce wani ne ya dora ta a hanya duk da damuwar da ta ke ciki. 

9. A shafi na 39, littafi na 3: An nuna duka ‘yan matan uku matsalar su daya, amma a zahirin labarin Farida ce kawai ta gamu da yaudarar samari, sauran biyun su su ka ja wa kan su ko kuma kaddarar su ce ta zo a haka. 

10. Bai kamata a ce lallai sai wani babban mai kudi ne ya auri Fauziyya ba; hakan zai sa wa makaranta (musamman ‘yan mata) dogon buri ko da sun yi kazamar rayuwa irin ta Fauziyya. 

11. Tun da Fauziyya ta tuba bai kamata a ce ta ci gaba da amfani da kadara ko dukiyar da ta samu ta hanyar haram ba. 

12. Babu lambar ISBN a littafin. 

Duk da haka, littafin ya yi dadi da ma’ana. A gaida Sa’a bocal.

Loading

Tags: Kaddarar Mu
Previous Post

Karatun Jami’a: Sai fa mun tashi tsaye!

Next Post

ABBA NA

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
ABBA NA

ABBA NA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!