SHUGABAN Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana baƙin ciki kan rasuwar shahararren ma’aikacin rediyo ɗin nan, Alhaji Kabiru Fagge, wanda ya rasu a Amurka a shekaranjiya Juma’a.
Mai ba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu a ranar Asabar a Abuja wadda mujallar Fim ta samu.
Ya ce: ”Fagge, ɗan shekara 77, suna ne wanda ya yi tambarin a duniyar Hausa saboda daɗewar da ya yi ya na aiki a Sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) har tsawon shekaru 25.”
Tinubu ya yaba wa gudunmawar da marigayin ya bayar ga aikin gina ƙasa, musamman ma dai wayar da kai da yekuwar da ya riƙa yi ta hanyar sanannen shirin sa na mako-mako kan harkar ilimi.
Ya ce: “Burin sa na taimaka wa al’umma ta hanyar aikin jarida ya faro ne tun a farkon rayuwar sa a matsayin ɗan rahoto mai bada gudunmawa a lokacin da ya ke koyarwa a makaranta. Mu na godiya da ayyukan da ya yi ta hanyar aikin da ya zaɓa wa kan sa da kuma kasancewar sa kyakkyawan jakada na Nijeriya a wannan babbar kafa ta duniya.”
Bugu da ƙari, shugaban ƙasar ya yi wa iyalan mamacin da kuma gwamnati da jama’ar Jihar Kano, har ma da dukkan masu aikin jarida ‘yan Nijeriya baki ɗaya ta’aziyya kan wannan rashi.