AURE ya yi albarka. Mai ɗaukar sauti a Kannywood, Bilal Muhammad Naseer (Lion) ya samu ƙaruwar ‘ya mace.
Amaryar sa Malama Jamila Isah Muhammad, ta haihu ne a daren Juma’a, 5 ga Janairu, 2024 a gidan sa da ke layin Mai Kala-Kala, unguwar Ɗirkaniya, Kaduna.
An raɗa wa jaririyar sunan mahaifiyar sa, wato A’isha, za a riƙa kiran ta da Halal.
Bilal ya shaida wa mujallar Fim cewa ya gode wa Allah tare da yin murna da samun ɗiya mace a matsayin ‘yar fari, saboda irin halaccin da mahaifiyar sa ta yi masa a duniya da kuma ya saka wa ‘yar sunan ta, duk da ba zai iya biyan ta abubuwan da ta yi masa a rayuwa ba.
An ɗaura auren Bilal da Jamila ne a ranar Asabar, 7 ga Janairu, 2023, a gida mai lamba L.I. 18, Fulani Road, kusa da Ramadan Hospital, Nassarawa, Kaduna.
Allah ya raya A’isha, ya albarkaci rayuwar ta.