• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Saturday, July 12, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nijeriya za ta haɗa gwiwa da Amurka wajen inganta ‘yancin ‘yan jarida da yaƙi da baza labaran bogi

by WAKILIN MU
September 19, 2024
in Nijeriya
0
Nijeriya za ta haɗa gwiwa da Amurka wajen inganta ‘yancin ‘yan jarida da yaƙi da baza labaran bogi

Minista Mohammed Idris tare da Jakada Richard Mills da Jibrin Baba Ndace (Shugaban VON) da Issa-Onilu (shugaban NOA)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana ƙudirin ma’aikatar sa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin ƙasar Amurka domin inganta ‘yancin manema labarai a Nijeriya.

Rabi’u Ibrahim, mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, ya faɗa a takardar da ya rattaba wa hannu cewa Idris ya faɗi hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wani zama da Jakaden Amurka a Nijeriya, Mista Richard Mills, a ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba.

Ministan ya ce: “Jakaden ya yi magana kan waɗansu abubuwa da yake ganin ya dace mu kula da su don inganta ‘yancin ‘yan jarida, mu kuma mun ba shi tabbaci kan irin abubuwan da muke yi, kuma ya ce ya san cewa muna yin abin da ya dace wajen tabbatar da cewa aikin jarida a Nijeriya ba kurum yana da cikakken ‘yanci ba ne, a’a har ma za a iya cewa yana daga cikin waɗanda suka fi ko’ina samun ‘yanci a faɗin duniya.

“Na san cewa akwai wasu ‘yan matsaloli nan da can, kuma muna aiki don kulawa da irin waɗannan wuraren don dukkan mu mu ci moriyar abin da ake kira ‘yancin aikin jarida, wanda muhimmi ne a kowace ƙasa mai da’awar mulkin dimokiraɗiyya mai ƙarko.”

Ministan ya nanata yadda gwamnatin Tinubu ta ba ‘yancin ‘yan jarida muhimmanci kuma ya tabbatar da cewa za ta ci gaba da inganta ‘yancin manema labarai a ƙasar.

Ya ce sun kuma tattauna kan yadda za su haɗa kai su yi aiki tare wajen yaƙar baza labaran bogi da na ƙage a ƙasar.

Ya ce: “Ya yi magana kan labaran bogi da na ƙage da na ƙarya, duk waɗannan abubuwan mun tattauna kan su. Dukkan mu mun yi amanna da cewa babu yadda za a yi ka gina al’umma ingantacciya a yayin da kake yaɗa labaran ƙarya kuma ba ka ɗauki batun labaran bogi da na ƙage da gaske ba.”

A nasa jawabin, Jakada Mills ya ce zaman da suka yi da ministan sun yi shi ne domin su tattauna kan hanyoyin ƙarfafa dangantakar da ke akwai tsakanin gwamnatin Amurka da ma’aikatar, musamman abin da ya shafi ‘yancin ‘yan jarida da haƙƙoƙin manema labarai.

Ya yi la’akari da ƙoƙarin da ministan ke yi wajen haɓaka ‘yancin ‘yan jarida da haƙƙoƙin manema labarai a Nijeriya.

Jakaden na Amurka ya yi la’akari da babban ƙalubalen da matsalar baza labaran bogi ke janyowa, musamman ga ƙasashen da ke tafiyar da mulkin dimokiraɗiyya a faɗin duniya.

Ya ƙara da cewa sun kuma yi musayar ra’ayi da shawarwari kan yadda za a magance ƙalubalen.

Loading

Previous Post

Bukar Maikaset Kasuwar Barci ya rasu

Next Post

Jarumar Kannywood Zulai Bebeji da ‘yan ƙungiyar ta sun fice daga sheƙar Kwankwasiyya sun koma ta Maliya

Related Posts

Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano
Nijeriya

SHEKARA ƊAYA BAYAN KOMAWA KAN KARAGAR MULKI: Tasirin Yadda Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Dawo Da Martabar Masarautar Kano

July 5, 2025
Next Post
Jarumar Kannywood Zulai Bebeji da ‘yan ƙungiyar ta sun fice daga sheƙar Kwankwasiyya sun koma ta Maliya

Jarumar Kannywood Zulai Bebeji da 'yan ƙungiyar ta sun fice daga sheƙar Kwankwasiyya sun koma ta Maliya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!