• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumar Kannywood Zulai Bebeji da ‘yan ƙungiyar ta sun fice daga sheƙar Kwankwasiyya sun koma ta Maliya

by MUKHTAR YAKUBU
September 23, 2024
in Labarai
0
Jarumar Kannywood Zulai Bebeji da ‘yan ƙungiyar ta sun fice daga sheƙar Kwankwasiyya sun koma ta Maliya

Hajiya Zulai Muhammad Bebeji (a tsakiya) tare da Sanata Barau Jibril a ofishin sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

 

ƘUNGIYAR Matan Mu A Yau da ta ƙunshi wasu jaruman Kannywood mata ta bayyana cewa ‘ya’yan ta sun fice daga tafiyar siyasar Kwankwasiyya a Jihar Kano, sun koma sheƙar jam’iyyar APC ɓangaren Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibril, wanda ake yi wa laƙabi da Maliya.

Shugabar ƙungiyar, Hajiya Zulai Abdullahi Bebeji, ita ce ta bayyana hakan ga mujallar Fim bayan dawowar su daga Abuja inda suka yi zama na musamman da Sanatan wanda ake sa ran zai yi takarar zama gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2017.

A bayanin ta, Hajiya Zulai ta ce sun bar Kwankwasiyya ne domin duk abubuwan da ke faruwa suna jin labari ne kawai, ba su san ma ana yi ba, duk da yake shekaru masu yawa da suka shafe sun hidimta wa tafiyar, amma da aka kafa gwamnati sai wasu masu shan kai suka hana su damar zuwa wajen da za a gan su a ji koken su har ma a san da su.

A ƙarshen makon jiya ne ƙungiyar ta samu gayyata daga ofishin Sanata Barau da ke Abuja, inda jagororin ta suka je suka gabatar da kan su a matsayin waɗanda suka rungumi tafiyar sa.

Sun sanar da shi manufofin su da ƙarfin da suke da shi da kuma gudunmawar da suke bayarwa a cikin harkar siyasa wadda ta taimaka wajen samun nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a zaɓe.

Hajiya Zulai Bebeji, wadda fitacciyar jaruma ce, ta ce duk da abin da suka yi a Kwankwasiyya ba a ga irin ƙoƙarin su ba, “don haka ne muka ga zaman mu a wajen ba shi da amfani.”

A hirar da ta yi da mujallar Fim, ta ce, “A lokacin da aka gan mu ana cire mana jan mayafi da wasu maza su ce wannan kuma me ta yi a tafiyar Kwankwasiyya?

“Amma dai mun yi tafiya ta Kwankwasiyya, mun kai mun komo wajen bayar da gudunmawa da ƙarfi na da kuma ƙungiyar da nake jagoranta.

“Amma dalilin da zai sa ba a san ni ba shi ne waɗanda nake yi wa ƙoƙarin ba su yarda sun kai ni inda za a ga abin da nake yi ba, don haka kullum nake yin tsalle ina direwa a waje ɗaya.

“Don ina tabbatar maka na yi tafiyar Kwankwasiyya tun a 2019, kuma duk abubuwan da suka faru da mu aka yi, wanda kowa ya san abubuwan da suka faru, wanda aka murɗe zaɓen.

“Kuma haka muka ci gaba da tafiya har aka zo wannan lokaci da Allah ya sa muka kafa gwamnati, wanda muke ganin tamu ce.

“Amma yadda muke da mutanen da muka shafe tsawon lokaci muna gwagwarmayar da su a yanzu sai suka yi mana katanga da gwamnatin yadda za a ji a ga ƙoƙarin da muka yi.

“Don haka duk wani abu da za a yi sai ya zama an mayar da mu gefe, idan ma wani abu ne ya taso za a yi da ‘yan fim mu sai dai mu ji ana yi.

“Kuma duk abubuwan da za mu yi na cigaban wannan gwamnati idan mun kawo sai waɗannan mutanen su hana mu kai inda ya kamata a ji a san da mu.

“Wannan ta sa na ga ba a damu da mu ba, ba a ma san da zaman mu ba, dole ne mu nema wa kan mu mafita.

“Don haka ne muka koma tafiyar APC gidan Sanata Barau Jibril, domin mun ga yana da son cigaban Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

“Kuma muka je ofishin sa a Abuja, ya karɓe mu hannu biyu, ya yi mana alƙawarin kulawa da mu tare da jin ra’ayin mu na siyasa domin akwai gudunmawa da za mu bayar.

“Kuma mu ma mun yi masa alƙawarin tafiya tare da kuma bayar da gudunmawa ta duk inda ake buƙata.

Sanata Barau Jibril tare da su Hajiya Zulai Bebeji a ofishin sa

“Don haka mu a yanzu ƙungiyar matan Kannywood tafiyar Sanata Barau Jibril muke yi. Ita za mu yi saboda manufofin sa na cigaban rayuwar al’umma sun yi daidai da manufar tafiyar ƙungiyar mu.

“Muna fatan Allah ya yi mana jagora ya kawo mana cigaba a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa wannan mataki da waɗannan matan na Kannywood suka ɗauka ba abin mamaki ba ne a yanzu da yanayin siyasar ƙasar nan yake sauya salo na kama abokin tafiyar da za a gudu tare a tsira tare.

Da ma ‘yan fim haka abin yake ta yadda kowa yake neman hanyar da za ta ɓulle masa.

Sauya sheƙar siyasa a wajen ‘yan fim ba sabon abu ba ne saboda kallon da ake yi masu na ‘yan kasuwar siyasa.

Sai dai kuma wasu za su yi mamaki ganin cewa ‘yan Kannywood suna da kyakkyawar alaƙa da gwamnatin Jihar Kano ta Kwankwasiyya, ganin yadda gwamnatin take cike da ‘yan fim masu riƙe da muƙamai.

Loading

Tags: Abba Kabir Yusufjarumai mataKwankwasiyyamatan KannywoodSanata Barau Jibrilsiyasasiyasar KannywoodZulai Bebeji
Previous Post

Nijeriya za ta haɗa gwiwa da Amurka wajen inganta ‘yancin ‘yan jarida da yaƙi da baza labaran bogi

Next Post

Gwamnatin Kano ta kulle gidajen kallo biyu saboda ƙin bin ƙa’idojin ta

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Gwamnatin Kano ta kulle gidajen kallo biyu saboda ƙin bin ƙa’idojin ta

Gwamnatin Kano ta kulle gidajen kallo biyu saboda ƙin bin ƙa'idojin ta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!