TSOHUWAR jaruma a Kannywood, Hajiya Halisa Muhammad, ta bayyana dalilin ta na kafa wata sabuwar ƙungiya ta wayar da kan mata a kan cutar sankarar mama.
A turance sunan ƙungiyar Women for Cancer Early Detection and Treatment Foundation, wato Gidauniyar Gano Kamuwa da Cutar Sankara da Wuri Tare da Magancewa.
Ƙungiyar ta yi nisa da wayar da kan mata tare da samar masu gudunmawa kan yadda masu larurar za su ci gaba da gudanar da rayuwar su a cikin yanayin da suka samu kan su.
Halisa, wadda a yanzu take kan shan magani tare da samun kulawar likita domin ceto rayuwar tata rayuwar daga larurar sankarar mama, ta faɗa wa mujallar Fim farkon tunanin ta na samar da ƙungiyar.
Ta ce: “To kamar dai yadda aka san ni, ni ‘yar Kannywood ce sama da shekaru 26, don zan iya cewa da mu aka kafa Kannywood ɗin. Kuma mace ce ni wadda na yi aure sau biyu. Ina da yara. Alhamdu lillah, kuma har yanzu ana cikin gwagwarmayar rayuwa kala-kala, kuma ni ‘yar kasuwa ce.
“Mafarin samar da ƙungiyar wayar da kai ta masu ciwon sankarar mama ta samo asali ne daga ciwo ne da ni na fuskanta. Na shiga cikin larura ta ciwon sankarar mama, kuma na samu ilimi a kan abubuwan da suke cikin ta.
“Don haka sai na ga a matsayi na na tsohuwar jaruma ya kamata na yi yekuwar wayar da kai a kan sankarar mama, don murya ta za ta je wajen da ta wasu ba za ta je ba. Saboda haka na ga ya kamata na kafa ƙungiyar don muryar mu ta je inda za a taimaka wa masu wannan larurar ta sankarar mama. Saboda cutar ta na da tsananin wahala da kuma kashe kuɗi, ga kuma tana saka damuwa, don haka cutar tana da tsananin da duk wani mai tunani in dai ba ya samu kan sa a ciki ba to ba zai taɓa gane me ake nufi ba.
“Wannan ya sa na ga ya kamata na ga na yi iya yadda zan iya na taimaka wa mutane, kamar yadda ni ma aka taimake ni. Saboda taimakon mutane da kuma gwamnati, da masoya na gabas da yamma, kudu da arewa, har na samu aka zo ga wannan lokacin.
“Kuma gaskiya a wajen faɗi-tashi wajen samuwar ƙungiyar, tunanin farko da na yi shi ne a kan me za a yi, kuma da wane irin kalami za a je wa da mutane?
“To sai na ga ina da masaniya a kan cutar sankarar mama ɗin, don haka sai muka nemo suna daga wannan ɓangaren, har aka tsayar da wannan sunan da muke kiran ƙungiyar a yanzu.
“Kuma muna wayar da kan mata ne a kan yadda za su gano cutar da wuri don a samu mafita. Kuma a yanzu har an yi wa ƙungiyar rajista.”
Da wakilin mu ya ce mata da yake ciwon na mata da maza ne, me ya sa ta fi mayar da hankali a kan wayar da kan mata, sai Halisa ta amsa da cewa: “To gaskiya mata su ne abin tausayi, sannan kuma sankarar mama tana ƙara ci ne kamar wutar kara, don idan ka je asibiti abin zai ba ka tausayi, za ka ga yara ƙanana ‘yan shekaru 16 zuwa 18 an yanke mata nono, ba manya ba ne. To ka ga dole ana buƙatar a wayar da kan mata don su gane ciwon ma akwai shi kuma gaskiya ne.
“Kuma masu ciwon sankarar mama suna cikin wani hali wanda ba zai misaltu ba, saboda yanayin kula da lafiya da kuma magani, da abincin da za a ci abubuwa ne masu wahala, don ba ƙaramar kulawa suke buƙata ba. Duk abin da kika mallaka da na dangin ki sai ya kusa ƙarewa a kan wannan cutar wajen ceto rayuwar ki, don haka ana cikin damuwa .
“Kuma asibiti nan ne inda matsalar take, domin mu za ka ga a kowace jiha asibitin koyarwa a nan ake duba masu rashin lafiya sankarar mama ɗin. To mu dai a nan Jihar Kano, muna roƙo ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya taimaka mana a kan kayan gwaje-gwaje da sauran ayyukan da ake yi wa masu wannan cutar, don ba mu da injinan, har sai mun tafi wata jihar, wani lokacin mu tafi Abuja ko Maiduguri da Sokoto, sannan ake yi mana aikin.
“Kuma aƙalla shi wannan ciwon ana ɗaukar shekaru uku zuwa huɗu ana ƙarƙashin kulawar likita, wasu ma har ya kai shekaru goma suna shan magani, don haka duk wanda ciwon nan ya same shi, ya samu kan sa a cikin wata babbar jarabawa. Sai dai mu roƙi Allah ya yaye mana wannan matsalar da muke ciki.
“Amma fa ciwon sankarar mama yana nan ƙauye da birni fiye da yadda ba ka zato. Wannan ne ƙarfin kafa ƙungiyar don ta shiga har ƙauyuka wajen wayar da kan mata a wayar masu da kai a nuna masu ciwon sankarar mama gaskiya ne. Idan a baya ana yin magungunan gargajiya yana tafiya, a yanzu ba haka ba ne. Zuwa asibiti a yanzu shi ne mai muhimmanci don a yi gwaje-gwaje a gano kina da shi, yadda za a ɗora ki a kan allurai da magani har a ga an cimma inda ake so a je.”
Mujallar Fim ta tambaye ta yadda suke samar da kuɗaɗen tafiyar da ƙungiyar, sai ta ce, “To a yanzu ni dai farko na sadaukar da kai na da rayuwa ta da lokaci na gaba ɗaya saboda masu cutar. Duk abin da na ke yi a yanzu su na ke tunawa, don ko abinci na ke ci sai na tuna.
“Don akwai masu larurar da abinci ma ya gagare su samu. Don haka a yanzu mutanen da suka saba taimakawa su ne dai za mu koma wajen su don su ci gaba da taimaka wa masu wannan larurar, domin suna buƙatar kayan abinci, magani, kuɗi na sayen allurai, haka nan suna buƙatar jini.
“Don haka muna neman taimako daga masu taimako da jini su je asibiti su ba da jini su ce wannan na masu ciwon sankarar mama ne. Saboda ciwo ne da yake shan jini fiye da tunani. Don haka muke buƙatar taimako.
“Kuma muna buƙatar gwamnati da ta ɗauke mana nauyin wasu gwaje-gwaje da ake yi mana, a ce kyauta ne. Idan an yi hakan ba ƙaramin adalci aka yi mana ba. Don shi wannan akwai wanda za ka ga wani dubu ɗari da hamsin, dubu ɗari biyu kuma kowanne da irin kalar magunguna da allurai da yake buƙata.
“Ka ga idan gwamnati ta ɗauke mana wannan, to an ɗauke mana abu mai nauyi a ciki, saboda shi wannan aikin duk bayan sati uku ake yi, kuma duk ranar da za a yi maka wannan aikin bayan ka sayi allurai da kayan gwaje-gwaje, za a fita ne da sassafe ƙarfe shida kana asibiti, don ka bi layi, kuma ba za ka dawo daga wannan gwajin ba tun da safe sai yamma wanda za a ɗauki tsawon shekara guda ana yi, sannan kuma sai a ɗora mara lafiya a kan gashi, sati uku-uku. Wasu za a yi masu sau takwas, wasu har sau goma, har zuwa sha biyu. Ya danganta da yanayin ƙonewar ciwon a jikin jini.
“Matsalar kayan gashi ba mu da shi a nan Jihar Kano. Akwai kuma wani gwaji da in an gama ake saka mutum a inji a ga da ciwon ko babu. To shi babu shi ma a Arewa gaba ɗaya, sai a Legas.
“Duk waɗannan matakai sai an bi wajen ceton marar lafiyar. Don haka muna neman taimako daga masu kuɗi da ƙungiyoyin ba da tallafi da kuma gwamnatocin jihohi da na Tarayya da su bayar da gudunmawa domin wayar da kai da kuma kulawa ga masu ɗauke da wannan cuta ta sankarar mama da take addabar mutane, musamman mata da suke raunana.”