Sakamakon gasar rubutun ƙirƙirarrun labarai na Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha zagaye na farko ya fito.
Sakamakon ya fito ne bayan tantance waɗanda suka yi nasara a zango na farko a gasar har kimanin mutum 50 cikin 126 da suka shiga gasar domin a fafata da su.
A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya sanyawa hannu, wannan sunayen da Hukumar ta saki daga na 1 zuwa na 50 ba yana nufin duk wanda ya ga sunan sa a kan layin na farko shi ne ya yi nasara ko kuma na hamsin shi ne ya zo a matsayin na ƙarshe ba.
Hukumar za ta bayyana sunan waɗanda suka yi nasara a nan gaba wato daga na 1 zuwa 3 sai na 4 zuwa na 15 inda kuma za ta bayyana wanda ya zo a matsayin na 16 zuwa na 50.
Sanarwar ta ƙara da cewa dukkannin waɗannan sunayen da Hukumar ta bayyana su ne a matsayin waɗanda suka yi nasara.
Haka kuma, kowa zai samu kyauta daidai da ƙwazon sa inda aka tsara ba da kyaututtuka kamar haka:
1. Na farko Naira Dubu Dari Biyar (#500,000)
2. Na biyu Naira Dubu Dari Uku (#300,0000)
3. Na Uku Naira Dubu Dari Biyu(#200,000)
4. Yayin daga kan na 4 zuwa na 15 za a ba su kyautar Naira Dubu Talatin (#30,000)
5. Sai Kuma rukunin karshe wato daga kan na 16 zuwa na 50 Hukumar za ta ba su kudin alkalami har Naira Dubu Goma Sha Biyar (#15,000).
Don haka ne Hukumar take jan hankalin waɗanda ba su samu kyauta ba da su tara a gasar da za a ƙara sakawa nan gaba, tare da yi misu fatan nasara.