TSOHON Editan mujallar Fim kuma fitaccen jarumi a Kannywood, Malam Aliyu Abdullahi Gora II, zai aurar da ‘yar sa ta biyu, wato Zainab.
Za a ɗaura auren ta da sahibin ta, Sadiq Ahmad, a ranar Juma’a, 28 ga Disamba, 2024 da misalin ƙarfe 1:30 na rana, bayan sallar Juma’a a Masallacin Juma’a na Marigayi Abubakar Mahmud Gumi da ke Malali Low-Coast, Kaduna.
Malam Aliyu ya nemi da a yi wa ma’auratan addu’a ga duk wanda bai samu damar halarta ba.
Allah ya kai mu ranar da rai da lafiya.