TSOHUWAR Shugabar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj, tana ɗaya daga cikin waɗanda aka karrama a Bikin Baje Kolin Finafinan Harsunan Afrika, karo na biyu (AILFF’24).
An gudanar da bikin karramawar ne a ranar Asabar, 14 ga Disamba, 2024 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, a filin wasa na Amphitheater Film Village, da ke Titin Anwai a garin Asaba da ke Jihar Delta.
Jagora kuma wanda ya kafa bikin baje kolin, Osezua Stephen-Imobhio, ya tura wa Lamaj saƙon sanarwa da taya ta murna, yana mai cewa, “Muna farin cikin sanar da ke cewa an zaɓe ki don samun lambar yabo a Bikin Baje Kolin Finafinan Harsunan Afirka na biyu (AILFF’24). Muna taya ki murna.”

A tattaunawar ta da mujallar Fim, Hajiya Fatima Lamaj ta nuna matuƙar farin ciki da wannan karramawa da ta samu na Life Time Achievement Champion Award, inda ta ce, “Ina miƙa godiya ga Allah da ya ba ni wannan dama na samun karramawa daga African Indigenous Language Film Festival.
“Wannan ba ƙaramin nasara ba ne a rayuwa. Ina godiya ga dukkan waɗanda su ka shirya wannan biki. Allah ya ba su nasara a kan dukkan abin da suke nema.
“Na gode ƙwarai da gaske.”