• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

by MUKHTAR YAKUBU da IRO MAMMAN
December 20, 2024
in Ranar Murna
0
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

Dakta Bilkisu Yusuf Ali da ɗiyar ta, Sarra, rungume da jariri Muhammad Tasi'u

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DAƊI biyu ya lulluɓe marubuciya Bilkisu Yusuf Ali a wannan makon, yayin da ta samun jika, sannan kuma ta samu digiri na uku wanda ake kira digirin digirgir ko dakta.

Kamar yau ne aka yi bikin ‘yar Malama Bilkisu ɗin, wato Sarra Tasi’u Ya’u Babura. Bisa yardar Allah a shekara guda da yin auren sai ga shi Allah ya albarkaci auren da ƙaruwa.

A ranar Talata, 10 ga Disamba, 2024 Sarra ta haifi ɗa namiji, wanda aka raɗa wa sunan Muhammad Tasi’u Salihu, wato sunan mahaifin ta.

Maijego Sarra riƙe da jaririn ta
Maijego Sarra tare da maigidan ta Salisu rungume da jaririn su

A ranar Laraba aka yi bikin raɗin sunan a gidan mahaifin jaririn da ke Tudun Yola a cikin garin Kano.

‘Yan’uwa da abokan arziki sun halarta domin taya murna.

Sarra tare da ‘yan’uwan ta na jini a wajen bikin
Maijego a tsakiyar marubuta mata

Mahalartan sun haɗa da rubuta irin su Sadiya Garba Yakasai, Lubabatu Ya’u, Hadiza Nuhu Gudaji, Bushira Nakura, Asma’u Sani, Hauwa Lawan Maiturare, Fauziyya D. Sulaiman, Halima Kurmin Mashi, da Fadila Aliyu.

A jiya kuma Bilkisu, wadda Malama ce a Jami’ar Alqalam da ke Katsina, ta kare kundin bincike da ta yi na zama dakta.

An yi zaman ne a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina, inda a nan ne ta yi karatun ta na digiri na uku.

Dakta Bilkisu riƙe da kundin binciken ta na dakta jim kaɗan bayan ta tsallake siraɗin kare kan ta dangane da shi a Katsina
Malama Bilkisu tare da malaman ta a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua a Katsina bayan zaman da suka yi da ita

Bayan an tabbatar mata da nasara a zaman, sai Dakta Bilkisu ta hau Facebook inda ta bayyana farin cikin ta, har tana tunawa da yadda mahaifin ta, marigayi Dakta Yusuf Ali, zai ji inda yana raye ta samu wannan gagarumar nasara.

Ta ce: “Allan ne kaɗai ya san irin farin cikin da Malam zai yi a yau da yana raye.”

Ta ƙara da cewa: “A yau, Malam na cika ma burin ka na kammala Ph.D (digiri na uku) cikin nasara a ɓangaren Adabi daga Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina.

“A ci gaba da hutawa, Imamu na; muna tare da kai da duk abin da kake so.
Dr. Bilkisu Yusuf Ali.”

Wannan muhimmin zango ne Hajiya Bilkisu ta kai, domin kuwa ta ɗan jima tana wannan karatu na zama dakta, har wasu na hangen ƙila ba za ta kai labari ba.

Ɗimbin jama’a sun taya ta murnar wannan sabon matsayi da ta samu a fagen ilimi.

Loading

Tags: Bilkisu Yusuf Alidigirin digirgirhaihuwajikaSarra Tasi'u Ya'u Ɓaɓura
Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba da tsarin Tinubu kan raya albarkatun kiwo da samar da abinci

Next Post

Sayyada Fati Bararoji za ta yi taron Mauludi tare da naɗin halifancin ta

Related Posts

Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

July 16, 2025
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai yi aure ranar Asabar

July 10, 2025
Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Next Post
Sayyada Fati Bararoji za ta yi taron Mauludi tare da naɗin halifancin ta

Sayyada Fati Bararoji za ta yi taron Mauludi tare da naɗin halifancin ta

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!