• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai kan nasarori, ta nemi ƙarin kasafin kuɗi na musamman ga ma’aikatar

by WAKILIN MU
January 14, 2025
in Nijeriya
0
Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai kan nasarori, ta nemi ƙarin kasafin kuɗi na musamman ga ma’aikatar

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da shugabannin hukumomin ma'aikatar sa a yayin bayyanar su a gaban Kwamitin Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai na Majalisar Tarayya domin kare kasafin kuɗi.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAJALISAR Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, bisa ƙoƙarin sa wajen gudanarwa da yaɗa bayanai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

An yi masa wannan yabon ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai don kare kasafin kuɗin ma’aikatar sa na shekarar 2025.

Sanatocin sun jinjina wa ƙoƙarin ma’aikatar amma sun nuna damuwa kan ƙarancin kuɗaɗen da aka ware mata, suna masu cewa ba zai wadatar ba don aiwatar da aikin ta na yaɗa labarai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Sun buƙaci a samar da ƙarin kasafin kuɗi na musamman domin a ƙarfafa wa ma’aikatar gwiwa.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP-Kogi) ta jaddada bambancin kasafin kuɗin ma’aikatar da na ƙasar Afirka ta Kudu, inda ta bayyana cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Afirka ta Kudu ta samu kimanin naira biliyan 409 don aiwatar da shirye-shiryen ta.

Ta ce Nijeriya, wadda ke da yawan al’umma fiye da waccan ƙasar, ya kamata ta ware ƙarin kuɗi don shirye-shiryen ta na yaɗa labarai.

Ta kuma jaddada muhimmancin wayar da kan al’umma, musamman matasa, da kuma yadda ministan da tawagar sa suke shirye don aiwatar da hakan idan aka ƙara masu kuɗi.

Shi kuwa Sanata Abdul Ningi (PDP-Bauchi) ya yaba wa ministan bisa ƙwarewar sa, jagorancin sa, da kuma cigaban da aka samu a hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar, musamman ta fuskar cigaba da aka samu a Hukumar Tlabijin ta Nijeriya (NTA).

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin, Sanata Ken Eze (APC-Ebonyi), ya buƙaci ma’aikatar da ta ƙirƙiro hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Ya kuma buƙaci a sake duba kasafin kuɗin, yana mai jaddada muhimmancin ɓangaren yaɗa labarai ga nasarar gwamnati.

Ya ce: “Ba za a iya yin abubuwa da yawa ba idan babu kuɗaɗen shiga, kuma bayanai suna da matuƙar muhimmanci: muna buƙatar ɓangaren ya jagoranci manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

“Kasafin kuɗin da ke gaban mu ba abin alfahari ba ne, idan an yi la’akari da abin da ake yi a wasu ƙasashe.

“Dole ne mu yi magana a matsayin ‘yan majalisa; dole ne mu ƙi amincewa da kasafin kuɗin ta hanyar kiran a ƙara yawan kasafin da aka ware wa ma’aikatar.

“Muna so Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Ƙasa ya bayyana a gaban mu don sake duba kasafin kuɗin.”

A baya, ministan ya ƙiyasta cewa mafi ƙarancin adadin da ake buƙata don gudanar da ayyukan ma’aikatar yadda ya kamata ya kai naira biliyan 50.

Loading

Tags: kasafin kuɗiMajalisar DattawaMohammed IdrisSanata Ken Eze
Previous Post

Zaɓen MOPPAN: Kwamiti ya fitar da tsarin yadda za a yi babban taro da zaɓe a Nassarawa 

Next Post

Ba mu buƙatar amincewar Sanusi kan tsare-tsaren mu na tattalin arziki, inji Ministan Yaɗa Labarai

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu a turereniya, ta ba da shawara kan bukukuwan Kirsimeti 

Ba mu buƙatar amincewar Sanusi kan tsare-tsaren mu na tattalin arziki, inji Ministan Yaɗa Labarai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!