• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result

  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen MOPPAN: Kwamiti ya fitar da tsarin yadda za a yi babban taro da zaɓe a Nassarawa 

by ALI KANO
January 9, 2025
in Labarai
0
Zaɓen MOPPAN: Kwamiti ya fitar da tsarin yadda za a yi babban taro da zaɓe a Nassarawa 

MOPPAN logo

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KWAMITIN Zaɓe na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ya fitar da tsarin yadda za a gudanar da babban taro da kuma zaɓen ƙungiyar a Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa, a ranar Asabar, 18 ga Janairu, 2025.

A cikin sanarwar musamman da ya fitar a yau, Sakataren kwamitin, Malam Ibrahim Ibrahim, ya ce ana sa ran dukkan wakilai masu kaɗa ƙuri’a, wato dalaget, da kuma ‘yan takara su isa garin a ranar Juma’a, 17 ga Janairu.

Ya ce za a tantance ‘yan takarar a dai wannan ranar ta Juma’a.

Sakataren ya ƙara da cewa washegari da safe, wato Asabar, za a yi babban taro tare da jin manufofin ‘yan takara da kuma zaɓe.

A tsarin, za a rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar da yamma a wannan rana ta Asabar, wato da ƙarfe 4.

Za a yi bankwana da juna tare da watsewa a ranar Lahadi, 19 ga wata.

Ibrahim ya ba da lambobin waya da mai buƙatar ƙarin bayani zai iya kira ya yi tambaya, wato 08038690968 da 07069108030.

Sakataren ya ce: “Muna fatan a yi wannan muhimmin taro cikin nasara tare da kira ga dukkan dalaget da ‘yan takara da su fito baki ɗaya a yi komai tare da su.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an yi ta ƙila-wa-ƙala a kan yiwuwar yin taron a Jihar Nassarawa saboda ba a samu tabbacin ko gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin sa ba kamar yadda MOPPAN ta buƙata.

Sai a yau ne takarda ta fito daga ofishin Gwamna Abdullahi Sule inda ya ba da amincewar ɗaukar nauyin babban taron na MOPPAN a Lafiya.

Sakamakon haka ne kwamitin zaɓen ya fitar da tsarin yadda za a gudanar da taron da zaɓen, wanda haka ya saka farin ciki a zukatan ‘ya’yan ƙungiyar.

Loading

Tags: Ibrahim IbrahimJihar Nassarawazaben MOPPAN
Previous Post

Baɗala: Hukumar Tace Finafinai ta dakatar da jaruma Samha Inuwa kan zargin shigar banza da wallafa batsa

Next Post

Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai kan nasarori, ta nemi ƙarin kasafin kuɗi na musamman ga ma’aikatar

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai kan nasarori, ta nemi ƙarin kasafin kuɗi na musamman ga ma’aikatar

Majalisar Dattawa ta yaba wa Ministan Yaɗa Labarai kan nasarori, ta nemi ƙarin kasafin kuɗi na musamman ga ma’aikatar

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!