JARUMI kuma furodusa a Kannywood, Shariff Aminu Ahlan, zai aurar da ‘yar sa, Hassana Shariff Aminu Ahlan.
Za a ɗaura auren ta da sahibin ta Ahmed Bala (Godiya), da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Juma’a mai zuwa, 21 ga Fabrairu, a masallacin Juma’a na Tukuntawa da ke Titin Gidan Zu, a cikin garin Kano.

A saƙon gayyatar da Ahlan yake aikawa, ya ce, “Salam. Ina farin cikin sanar da ku ɗaurin auren ‘ya ta Hassana Shariff Aminu Ahlan.
“Za a ɗaura ranar Juma’a mai zuwa idan Allah ya kai mu. Idan ba a samu zuwa ba, a taya mu da addu’a.”