Firayim Ministan ƙasar Habasha, Abiy Ahmed, yana yi wa Shugaba Bola Tinubu da Uwargidan sa, Sanata Oluremi Tinubu, rakiya ranar Litinin a Babban Filin Jirgin Sama na Bole a birnin Addis Ababa bayan sun halarci Babban Taro na 38 na Ƙungiyar Haɗa Kan Afrika.