• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, November 1, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

by ABBA MUHAMMAD
July 15, 2025
in Nijeriya
0
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

Alhaji Yerima Shettima tare da wasu 'yan fim na Kaduna da suka ziyarce shi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
FURODUSA kuma jarumi a Kannywood, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa Alhaji Yerima Usman Shettima za su yi a takarar zama Sanatan mazabar Kaduna ta Tsakiya babu gudu, babu ja da baya.
Abdullahi ya yi wannan bayani ne a yayin da suka ziyarci Yerima wanda shi ne Shugaban na Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (AYCF) a ofishin sa da ke Kaduna a jiya Litinin.
Sauran abokan ziyarar sun haɗa Malam Musa Mohammed Abdullahi, Hajiya A’isha NTA da Raliya Muhammad.
Furodusan da muƙarraban sa sun bada himma wurin amfani da basirar su da kuma damar su don ganin sun isar da saƙon talakawan Kaduna ta Tsakiya ga Yerima Shettima domin ya amsa kiran su.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Abdullahi Abbas ya ce, “Muna godiya da samun wannan dama. Lallai mu a wannan tafiyar, mu muna kallon mutum wanda yake da ilimi, wanda ya cancanta.
“An kira ni wata tafiya, saboda abin da na yi wa Bello El-Rufa’i lokacin, kuma mun yi, an samu nasara. Kuma siyasar nan da za a yi a nan gaba, ba wai ka jingina da wani ba ne, wanene kai, in ka ce jingina da wani za ka yi, faɗuwa za ka yi. Kawai ka bari mutane su yarda da waye kai kawai, shi ne. Don haka wannan tafiyar babu gudu, babu ja da baya.”
Daga hagu: Alhaji Abdullahi Abbas da Malam Musa Abdullahi tare da Yerima Shettima a ofishin sa
A nasa ɓangaren, Yerima Shettima, wanda shi ne mijin tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan, ya yi masu barka da zuwa, sannan ya yi masu godiya da irin nuna masa ƙauna da suke yi, wanda ya ce ya tabbata suna yi ne ba don kuɗi ko wani abin hannun sa ba. Hakan ya sa ya neme su da su zo ya gan su, su gan shi.
Haka kuma ya tabbatar masu da cewa lallai shi ɗan gwagwarmaya ne, kuma ɗan gwagwarmaya idan ya samu dama, ya samu ‘power’, ya bambanta da wanda shi ɗan siyasa ne kawai, wanda shi yana kallon siyasar a matsayin jari ne kawai, ya zama ɗan jari hujja, shi kuɗi zai tara, ya yi abin da zai yi, ya yi gaba.
Ya ce, “To, ni shekara sama da ashirin gwagwarmaya nake yi a rayuwa ta, Arewa ba ta iya gane ni ba, sai da aka yi wannan maganar ba Inyamurai ‘quick notice’, wanda ni ma na ce Inyamurai su bar Arewa daga baya ya zo, amma rigimar OPC, in Allah ya yarda ni na kawo ƙarshen rigimar OPCC. Wanda yake da tarihi ya san wannan.
“Amma na yi abubuwa da yawa a Kudu, duk wanda yake ɗan Kudu zai iya bada tarihi na ya ce mun san shi, ga abin da ya yi mana lokacin. Daga nan kuma Allah ya dawo ni gida.
“Kuma aure ya sake dawowa da ni, don asali na ni ɗan Zariya ne, amma na yi karatu a Kudu, abin da ya kai ni Kudu kenan da kuma zama haka, na yi mata a can, sannan na sake dawowa na sake yin mata, amma yanzu na fi zama a nan.”
Ya ci gaba da cewa, “Mu riƙe juna da amana, ba don kuɗi ba, ba kuma don ina da kuɗin da zan saye ku ba, kowa da kuka gani a nan ‘voluntary’ ne yake yi. Amma in muka haɗa ƙarfi da ƙarfe da iya ƙarfin da Allah ya ba ni da kuma waɗanda za su zo su dafa mana, in-sha Allah za mu kai labari. In dai rabo namu ne, babu wanda ya isa ya hana mu sai Allah, ba dai mutum ba.
“Haka kuma, a tsarin mu ba tsaro kwata-kwata. Don haka ku saki jikin ku ku yi duk abin da za ku yi. Ba don kuɗi na neme ku ba, don da kuɗin ne aka nuna min ana so, ƙila ba zan yi sha’awar in gan ku ba, saboda ba ni da kuɗin da zan iya sayen kowa, domin ba na cikin gwamnati, duk abin da zan bada, daga cikin zufa na nake badawa. Ba ni da muƙami a cikin gwamnati, ban taɓa riƙe muƙamin gwamnati ba tunda Allah ya yi ni, yanzu nake nema. Na gode, Allah ya bar zumunci.”
Zaharadden Sani, Aisha NTA, Musa Abdullahi, Yerima Shettima, Abdullahi Abbas da sauran su a lokacin ziyarar
Aminin sa, wato Alhaji Shehu Sani Sado, shi ma ya tofa albarkacin bakin sa, inda ya ce, “Kamar yadda shugaban mu ya yi jawabi, inda ya ce ya fito takara, ba shi ya fito ba, mu muka matsa masa da ya fito.
“Yerima Shettima mutum ne da yake wa al’umma abubuwa ba tare da wani ya sani ba ko an yaɗa wa duniya ba, amma yanayi ne ya kawo mu na siyasa, wanda mun riga da mun bi, kuma muna so kowa ya ɗauke shi kamar yadda muka yi.
“Duk wanda yake yi domin Allah zai ga sakayya, ba wai sai mutum ya biya ka ba, in dai ka yi tafiyar nan tsakani da Allah babu yaudara a ciki, za ka ga sakamako mai kyau. Duk muna yi ne saboda da kishin al’ummar mu da kuma ci-gaba.
“Kuma wannan tafiyar in kana cikin ta, ba za ka taɓa yin da-na-sani ba in-sha Allahu. Kuma kamar yadda ya jaddada maku, ni ma zan ƙara jaddada maku. Wannan tafiya muna yin shi kai-tsaye ne. Duk da cewa ban san da zuwan ku ba, amma dai wannan ya nuna cewa an damu da ku, duk wanda ka yi masa abu, yana da damar ya yi godiya ko ya bar ka da abin ka. Don haka mu riƙe amana. Na gode.”
Hajiya A’isha NTA ita ta fara magana a cikin waɗanda suka kai ziyarar, inda ta ce, “Mu babban burin mu Allah ya kai ka inda ba mu taɓa tsammani ba. Allah ya tallafa mana. Duk wanda zai shiga tafiyar ka, Allah ya sa ya shiga da zuciya ɗaya, ya san cewa tafiyar da za mu yi, tafiya ce ta adalai, masu imani. Saboda shi kan shi wanda shi ne jagoran wannan tafiyar, mutum ne mai imani. Allah ya kai mu ga gaci, ya sa mu samu abin da muke so. Allah ya sa duk ranar da za mu yi irin wannan haɗuwar, mu yi haɗuwar farin ciki, a ce mun kai ga nasara, ne babban burin mu.”
Shi ko jarumi Malam Musa Mohammed Abdullahi cewa ya yi, “Ni abin da ya sa nake da ‘interes’ a kan ka, akwai abubuwa guda biyu. Wani lokaci a baya, ranar da aka rantsar da Zaharadden Sani a matsayin shugaban ‘yan wasa na Jihar Kaduna, mun yi ƙorafin cewa mu ‘yan fim idan rashin lafiya ya kama mu, ba mu da wata gidauniya da za ta tallafa wa mara lafiya. To, a wannan rana kai da Abdul Amart kuka bada N100,000. Wannan abin da ka yi, shi ya nuna cewa kana ƙaunar mu.
“Sai na biyu, akwai wani shaƙiƙi na ne, yana tare da Yusuf Zailani, sai ya ce min na riƙe wuta a kan ka, meye dalili? Na ce, na bar wa kai na dalili, sai ya ce ina ɓata lokaci na ne, sai na ce babu komai. Sai ya ce, ka bar can ka zo nan, na ce a bar ni in tafi inda nake so.
“Sai kuma aka shigo da wani yanka, wai ana so a sanar da ni, kai ba ka da sama, sai na ce, Allah shi ne saman ka. A ƙarshe dai na ce a tsarin harkar mu, duk inda aka neme mu za mu je mu yi aiki, amma mu mun san inda muke.
“Allah ya ba mu nasara. Kada a yi sanya ko a ce za a yi amfani da ‘yan sara-suka. Mun yi siyasa a lokacin Shagari. A wannan lokacin, an sa wani ya yanke ni, kuma ya yanke ni. Aka kama shi aka kulle, na sa aka fito da shi saboda wanda ya sa shi aboki na ne. Allah ya shige mana gaba.”
A ƙarshen taron, an yi addu’o’in neman nasara, zaman lafiya da haɗin kai.

Loading

Previous Post

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da babban kwamitin shirya taron masana’antun fasaha na Nijeriya

Next Post

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

Furodusa a Kannywood, Rabi'u Koli da A’isha sun zama ɗaya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!