GWAMNATIN Jihar Kano ta ƙaddamar da babban kwamitin da zai shirya gagarumin taron ƙasa kan amfani da masana’antar fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire domin haɓaka tattalin arzikin Nijeriya.
Wannan wani babban mataki ne na sake mayar da tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire a matsayin ginshiƙin cigaban ƙasa.
Da yake ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnatin jihar, Kwamishinan Yaɗa Labarai Da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa taron zai kasance wani kafaffen dandali ga manyan masu ruwa da tsaki don gano dabarun fasaha, ilimi, da ƙulla ƙawance da nufin ɗaukaka masana’antar fasaha ta Nijeriya zuwa ɗaukaka a duniya.
Kwamared Waiya ya jaddada cewa, “Taron zai haska hanyoyin fasaha da Kano take da su, da baje-kolin kayayyakin gargajiya, da yin hulɗa da kafafen yaɗa labarai na duniya da fitar da sanarwar da ake sa ran za ta jawo hankalin ƙasa da ma duniya baki ɗaya zuwa ga fannin.”
Waiya ya ce, “Taron yana wakiltar wani muhimmin cigaba a ƙoƙarin mu na haɗin gwiwa don ɓullo wa ɗimbin ƙarfin tattalin arzikin da ke tattare da ɓangaren fasaha na Nijeriya.”
Ya yi alƙawarin zama wurin taro “don inganta al’adun mu, ƙarfafa wa masu sana’a da kuma shiga cikin hazaƙa na mutanen mu don ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.”
Kwamishinan ya yaba wa Gidauniyar Kannywood bisa hangen nesan da ta yi wajen gabatar da batun taron, inda ya bayyana shi a matsayin wani ƙoƙari na yabawa wanda ya yi daidai da muradin cigaban jihar.
Waiya ya ƙara da bayyana goyon bayan da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, yake ba shi, wanda ya bayyana a matsayin jagora mai hangen nesa.
Ya kuma yi nuni da cewa gwamnan yana kallon taron a matsayin wata dama wadda ba kasafai ake samun ta ba wajen ƙarfafa wa haziƙai masu fasaha a Kano da ma sauran su gwiwa.
A cewar sa, “Ɓangaren fasaha yana da damar da zai samar da ayyukan yi, arziki, da ƙaruwar tattalin arziki ta hanyar amfani da kadarorin mu na al’adu da basirar ƙirƙire-ƙirƙire. Za mu iya buɗe sababbin iyakokin tattalin arziki ga matasan mu da ‘yan kasuwa.”
Kwamitin wanda kwamishinan yake jagoranta, ya haɗa da Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Ahmed Tijjani Auwalu, Kwamishiniyar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hajiya A’isha Lawan Saji, Gidauniyar Kannywood, babbar sakatariyar Hukumar Tarihi da Al’adu, Manajan Darakta na Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido ta Jihar Kano, Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, wakiliyar Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin fasahar intanet (ICT), shugaban Ƙungiyar Daraktoci ta Nijeriya, wakilin Ƙungiyar Masu Sana’o’i, wakilan Ƙungiyar Masu Sana’a da Fasaha, wakilan Ƙungiyar Masu Sana’o’in Hannu da wakilin Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA).
Sauran membobin sun haɗa da wakilin ofishin mataimakin gwamna, Malam Ibrahim Ado Kurawa, Farfesa Abdalla Uba Adamu, Hajiya Nabila Ibrahim, wakiliyar majalisar masarautar Kano, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tattara kuɗaɗen shiga, wakilin Hukumar Tara Haraji ta Kano (KIRS), da Dakta Ahmad M. Sarari.
Membobin sakatariyar sun haɗa da wakilin ofishin Majalisar Ministoci, wakilin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Usman Bello, Daraktan Harkokin Cikin Gida, da Ahmad Alkanawy.
Daraktan Ayyuka na Musamman a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano, Malam Sani Abba Yola, shi ne wanda ya fitar da sanarwar ƙaddamar da kwamitin.
![]()






