WATA kotun majistare da ke unguwar Nomansland a Kano a jiya ta tura wani matashi mai suna Umar Hisham Fagge, wanda aka fi sani da Tsulange, zuwa gidan yari bisa zargin sa da aikata baɗala.
Tsulange yakan tare titi yana wanka tare da saka rigar mama yana yawo, kuma yana wallafa bidiyon barkwanci wanda ke ɗauke da abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da alʼada da shari’ar Musulunci a shafin sa na “tsulangene back up”.
Kotun, a ƙarƙashin Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan, ta yi umurnin a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 3 ga Yuli, 2025.

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ce ta gurfanar da shi a kotun bayan ta kama shi da laifin ayyukan baɗala.
Hukumar tana ci gaba da ɗaukar irin wannan matakin domin yaƙar aikin rashin ɗa’a a soshiyal midiya a jihar.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin diddigin duk wani abu da ke iya dagula tunanin matasa, musamman masu amfani da soshiyal midiya suna sheƙe ayar su da sunan nishaɗi don neman suna.