• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, April 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

by MUKHTAR YAKUBU
August 24, 2025
in Taurari
0
Abin da ya sa aka daina gani na a Kannywood – Ummi Duniyar Nan

Ummi Abdulwahab (Ummi Duniyar Nan)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN shafe tsawon lokaci ba a ganin matashiyar jaruma Ummi Abdulwahab wadda aka fi sani da Ummi Duniyar Nan a cikin farfajiyar masana’antar Kannywood. Hakan ya sa wasu ke ta tambayar ina ta shiga ne?

Kwanan nan wakilin mujallar Fim ya haɗuwar da Ummi a Kano, inda ya nemi su tattauna game da dalilin rashin ganin nata.

A tattaunawar, jarumar ta bayyana mana tsawon lokacin da ta yi rabon ta da harkar fim da kuma abubuwan da suka sa aka daina ganin ta, kamar haka:

FIM: Ummi, kina cikin jarumai masu tasowa a shekarun baya amma lokaci guda sai aka neme ki aka rasa a harkar fim. Ko ina kika shiga?

UMMI DUNIYR NAN: To, ahamdu lillah. Kamar yadda ka faɗa, ina daga cikin jarumai masu tasowa a shekarun baya, haka ne. Don a lokacin da na shigo harkar, jarumai mata da suke tashe su ne su Hadiza Gabon, Halima Atete, da A’isha Tsamiya. Kuma jaruman da muka shigo harkar lokaci ɗaya da su su ne Rahama Sadau, Tumba Bubakar, saboda kusan lokaci ɗaya muka shigo; mutane sun yi ta surutu a kan ko wacece za ta sha gaban wata a cikin mu. To cikin ikon Allah a lokacin mun ci zamanin mu, mun yi tashe, duniya ta san mu dukkan mu.

FIM: Amma duk da wannan dama da kika samu a lokacin, daga baya sai aka daina ganin ki a cikin harkar fim. Ko me ya kawo hakan?

UMMI: E, gaskiya ina yin fim ba wai na daina ba ne. Sai dai abin da ya faru shi ne, a baya iya sana’ar fim kawai nake yi, shi ya sa aka fi gani na. Amma daga baya sai ya zama akwai wasu harkokin kasuwancin da nake yi har yanzu. Kuma a lokacin ba na shiga harkar siyasa, kuma daga baya na zo na shiga harkar siyasa, ina yin waƙoƙi da sauran wasu ayyuka na ‘yan siyasa, don haka sai hankali na ya rabu kashi-kashi. Amma dai duk abin da na zama shi dai wannan fim ɗin shi ne ya zamar mini sila, don haka ban yada harkar fim ba, duk lokacin da aka kira ni idan ina da lokaci zan yi.

Jaruma Ummi Abdulwahaf
Ummi Abdulwahab

FIM: To a yanzu wanne matsayin kike a harkar fim? Kin ja baya ne ko kina yin ta ne sai dai rashin lokaci?

UMMI: Ina yin fim har yanzu, ban ja baya ba, kuma ban daina ba, don ko a satin nan an kira ni mun je wani aikin. Don haka duk wanda yake buƙatar na yi masa aiki idan ya kira ni zan je mu yi aikin.

FIM: Ya za ki kwatanta harkar fim a yanzu da kuma lokacin da kuke tashe a baya?

UMMI: E to, ka san gaskiya komai yana tafiya da zamani. Amma harkar fim a yanzu da kuma a baya akwai bambanci sosai, an samu sauyi; wasu abubuwan za ka ga na cigaba ne, wasu kuma na cibaya; wani ma sai abin ya ba ka haushi. Don ka ga a baya ana yin fim ne a kai kasuwa, amma a yanzu ya koma onlayin. To ka ga cigaba ne, sai dai ta wani ɓangare ya taɓa harkar fim ɗin.

FIM: Ko kina da ra’ayin nan gaba ki zuba kuɗi ki fito da wani fim ɗin?

UMMI: To ai ko a can baya idan ka kula mata da yawa sun zuba kuɗi sun yi fim. Amma wajen da matsalar take, su mazan ne suke danne mu, don haka idan ba ka samu waɗanda za su taya ka ku yi aikin tare ba daga ƙarshe sai mace ta rasa inda kuɗin ya shiga. Wannan ta sa da dama mata suka haƙura da zuba kuɗin su don su yi fim.

FIM: A yanzu da duniya ta sauya, jarumai sun fi tashe a shafukan sada zumunta, amma Ummi Abdulwahab ba a cika ganin ta ba. Ko me ya sa hakan?

UMMI: Gaskiya haka ne, ka san kowa da irin nasa ra’ayin. Ba wai harkar soshiyal midiya ba ne ba na yi, amma ni da man tun a baya ban damu da sai na buɗa rayuwa ta a soshiyal midiya kowa yana gani ba, don wani lokacin irin wannan yana jawo wa mutum damuwa. Amma dai duk abubuwan da ake yi ina shiga ina kallo.

FIM: A matsayin ki na jarumar fim, ko kin cimma nasarar da kike buƙatar samu?

UMMI: Gaskiya Alhamdu lillah, ba yanzu ko da nan gaba, ban san abin da Allah zai yi mini ba. Tsakani na da harkar fim sai godiyar Allah. Duk wata nasara da nake nema na same ta a harkar fim.

FIM: Da yake kin fi bayar da ƙarfi ga harkar kasuwanci, ko ya kike haɗa harkar fim da kasuwanci?

UMMI: To ai wannan abu ne mai sauƙi, don ina yin talla ta onlayin, kuma muna da shagon da muka buɗe a kasuwar Kantin Kwari a Kano, duk wanda yake buƙata sai ya neme mu ta waya ko kuma a shagon mu. Don haka ba wani abu ba ne mai wahala. Harkar kasuwancin yanzu a cikin sauƙi ake yin ta, don haka harkar kasuwanci ba za ta hana ni yin fim ba. Duk da yake ni na fi tafiyar da kasuwancin ta onlayin, sai lokaci zuwa lokaci nake zuwa shagon. Don haka duk mai buƙatar sayen kaya na da suna shafi atamfofi, les, shadda, takalma da sauran kayayyaki, sai ya neme ni ta shafi na ko a lambar waya, zai same ni kai-tsaye.

FIM: Wane saƙo kike da shi ga sauran jarumai abokan sana’ar ki ta fim?

UMMI: Saƙo na shi ne su nemi sana’a, domin ita harkar fim lokaci ne, idan kina ganin a yanzu harkar tana yi da ke, to wata rana za ta daina yayin ki. Don haka ki samar wa kan ki mafita tun harkar fim tana yi da ke.

FIM: To, madalla, mun gode.

UMMI: Ni ma na gode sosai.

Loading

Tags: Duniyar Nanjarumai mataKannywoodUmmi Abdulwahab
Previous Post

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll ya buƙaci iyaye su saka ido kan finafinan da yaran su ke kallo

Next Post

MOPPAN ta yi zama da malamai don samun fahimta da ‘yan Kannywood

Related Posts

Jaruma Hauwa Musa Adam
Taurari

Ina son zama mai taimakon al’umma — jarumar Kannywood Hauwa Musa Adam

August 14, 2025
Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi
Taurari

Na fi so in fito a matsayin masifaffiya a fim, inji Fa’iza Abdullahi

December 25, 2024
Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’
Taurari

Fim ɗi na mai suna ‘Baban Ladi’ na ja sosai, inji sabon furodusa Razaki jarumin ‘Daɗin Kowa’

November 25, 2023
Sayyada Raihan Imam Ahmad (Ƙamshi)
Taurari

Fim riga ce ta arziki – Raihan Imam Ƙamshi

November 20, 2023
Saratu Abubakar
Taurari

Yadda ɗaukaka ta sa na ke rufe fuska – Saratu Abubakar

October 1, 2023
Safna Lawan
Taurari

Buri na a Kannywood ya kusa cika, inji Safna Lawan

August 24, 2023
Next Post
MOPPAN ta yi zama da malamai don samun fahimta da ‘yan Kannywood

MOPPAN ta yi zama da malamai don samun fahimta da 'yan Kannywood

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!