TUN tuni aka yi ittifaƙi da cewa da jaruman Kannywood na da matuƙar rawar da za su iya takawa wajen magance matsalar al’umma.
A yayin da ƙasar nan ta ɓarke da zanga-zangar fafutikar ganin sun magance matsalolin da ke damun su, an ga fuskokin mawaƙa da jarumai, ciki har da na masana’antar finafinan Hausa, waɗanda su ka fito domin a dama da su a gwagwarmayar da ake yi yanzu.
Hakan ya ƙara bayyana a yadda Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya A’isha Buhari, ta yi magana kan abin da ke damun ‘yan ƙasa.
A ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2020 Hajiya A’isha ta wallafa a shafin ta na yanar gizo cewa #achechijamaa, har ta saka wata waƙa da fitaccen jarumi Adam A. Zango ya yi kan matsalar ƙasa. Waƙar ta ƙunshi hotunan Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari da na manyan hafsoshin soja.
Sai dai a yau Uwargidan shugaban kasar ta sake magana a karo na biyu inda a wannan karon ta ce, “Arewa mu farka.”
Ta kuma saka waƙoƙin ‘yan Kannywood irin su Ali Nuhu, Ali Jita da Nazir Sarkin Waƙa, ta ƙara da hotunan zanga-zangar da su Ali Jita su ka yi.
Wannan ya ƙara nuna cewa ‘yan Kannywood su na da rawar da za su taka wajen share wa jama’ar da su ke wakilta hawayen su.