• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, November 2, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ministar Agaji ta ƙaddamar da shirin bada lamuni ga mata a Filato

by DAGA WAKILIN MU
October 18, 2020
in Nijeriya
0
Hajiya Sadiya Umar Farouq da Madam Pauline Tallen wajen miƙa buhunan abincin agaji daga Rumbun Abinci na Ƙasa, a Jos

Hajiya Sadiya Umar Farouq da Madam Pauline Tallen wajen miƙa buhunan abincin agaji daga Rumbun Abinci na Ƙasa, a Jos

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
A KARON farko, Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bada lamuni ga matan karkara, wato ‘Special Grant  for Rural Women’.
 
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta ƙaddamar da shirin a Jos, hedikwatar Jihar Filato.
 
A ƙarƙashin shirin, sama da mata 150,000 ne za a yi wa biya ɗaya rak na kuɗi N20,000 kowacen su a kowace daga cikin ƙananan hukumoni 774 da ke faɗin ƙasar nan.
 
A wajen ƙaddamar da sabon shirin wanda aka yi a ɗakin taro na Gidan Gwamnati a Jos, ministar ta ce biyan sau ɗaya ne za a yi wa mace don bikin tunawa da Ranar Matan Karkara ta Duniya (International Day of Rural Women). 
 
Sadiya ta ce: “Tun daga zuwan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a cikin 2015, gwamnati ta yi ta bada fifiko ga kula da halin da talakawa marasa galihu na ƙasar nan ke ciki tare da tallafa masu. Hakan ne ya sa aka yanke shawarar shigo da Shirin  Inganta Rayuwa na Ƙasa, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP) a matsayin wata dabara ta kyautata zamantakewar jama’a.
 
“An ƙirƙiro Shirin Bada Lamuni ga Matan Karkara ne domin a inganta manufar zamantakewa da gwamnatin Buhari ke da ita, wanda ya haɗa da buƙatar ceton ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara a cikin shekaru 10. An tsara shi yadda zai samar da biya ɗaya rak na lamuni ga wasu daga cikin matan da su ka fi kowa fatara a yankunan karkara na Nijeiya. 
 
“Za a raba kuɗi N20,000.00 ga mata masu fatara su sama da 150,000 a yankunan karkara da ke faɗin jihohi 36 na ƙasar nan da Yankin Birnin Tarayya.
 
“Ana sa ran kuɗin za su bada damar samun jarin yin sana’a wanda ake buƙata don hadahadar kasuwanci. 
 
“Fatar mu ita ce waɗanda su ka amfana da wannan shiri za su yi amfani da wannan damar wajen inganta kuɗin da su ke samu, da sama wa kan su abinci da kuma uwa-uba bada gudunmawa ga kyautata rayuwar su ta yau da kullum.”
 
Sadiya Umar Farouq ta kuma gode wa Ministar Harkokin Mata, Madam Pauline Tallen, saboda gudunmawar da ta bayar ga cimma nasarar ƙaddamar da shirin a Jihar Filato.
 
Haka kuma ta yi amfani da wannan damar ta raba hatsi iri daban-daban daga Rumbun Abinci na Ƙasa (National Food Reserve), bisa amincewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a matsayin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi waɗanda zaman dole na annobar korona ya shafa.
 
Kayan abincin da aka raba a jihar sun haɗa da tirela 71 shaƙe da masara, dawa da gero waɗanda za a ba gidaje 294,199.
 
Tun da farko, sai da Gwamnan Jihar Filato, Mista Simon Bako Lalong, ya bayyana matuƙar farin ciki ga ministar saboda ziyarar da ta kai a jihar. 
 
Ya yi nuni da rawar da mata ke takawa a cikin al’umma, musamman matan karkara.
 
Ya ce, “Wannan kayan agajin za su taimaki mutane marasa ƙarfi da annobar korona da sauran bala’o’i su ka shafa, irin su rikicin ɓangaranci da ambaliyar ruwa.
 
“Wannan taro dai na musamman ne domin kuwa ya ƙunshi raba kuɗin tallafi ga matan karkara 500 don tunawa da Ranar Matan Karkara ta Duniya.
 
“Haka kuma ina farin cikin ganin cewa ana ba mata masu ciki da masu shayarwa su 3,005 a Jihar Filato ƙarin naira dubu biyar kowacen su a shirin nan na tiransifar kuɗi bisa ƙa’ida, wato ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT). 
Sadiya Umar Farouq zaune tare da Gwamna Lalong a yayin da Pauline Tallen ke gabatar da jawabi a Gidan Gwamnati
“Hakan zai taimaka gaya wajen inganta rayuwar mata da ƙananan yara a Jihar Filato, musamman ta fuskar kiwon lafiyar su da ba su ƙarfin yin sana’a.”
 
Gwamna Lalong ya ce gidaje masu fatara guda 26,004 a jihar sun riga sun amfana da kuɗi N10,00 da ake biya sau biyu a wata a ƙarƙashin shirin CCT, a yayin da wasu gidaje 47,000 su na jiran a biya su. 
 
Ya ce jihar ta na da gidaje 231,870 a rubuce a Rajistar Al’umma ta Jiha. 
 
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta faɗaɗa shirye-shiryen ta na agaza wa al’umma don shigar da mutanen da su ke jira a rubuta su. 
 
Jigon Ranar Matan Karkara ta Duniya ta bana dai shi ne “Gina Jimirin Matan Karkara a Zamanin Annobar Korona”, wato ‘Building Rural Women’s Resilience in the Wake of COVID-19”.

Loading

Previous Post

Al’ummar Barwa sun yaba wa minista Sadiya saboda rijiyar burtsatse da asibiti

Next Post

Yadda Aisha Buhari ta hasko tasirin ‘yan Kannywood a gwagwarmayar ceton talakawa

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Hajiya Aisha Buhari tare da Adam A. Zango da Nazir Ahmad Sarkin Waƙa

Yadda Aisha Buhari ta hasko tasirin 'yan Kannywood a gwagwarmayar ceton talakawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!