WADANNAN wasu daga cikin hotunan liyafar cin abincin dare ne (dinner) ta auren fitaccen jarumin Kannywood Mustapha Mustapha (Musty) da kyakkyawar amaryar sa, Ghadir Mahmud Shareef (Soha), wadda aka gudanar a daren yau a Kano.
Gobe Lahadi, 29 ga Nuwamba, 2020 za a ɗaura auren su a gidan Alhaji Ibrahim D.O. da ke daura da gidan Nababa Badamasi a Titin Jakara, Goron Dutse, Kano.

Ga amarya da ango nan a cikin masoyan su, duk sun haske wurin walimar.





