ƊAYA daga cikin mata dattawa a masana’antar Kannywood, Hajiya Ladi Haruna, wadda ake kira Ladin Cima ko Tambaya, ta waiwaya baya a rayuwar ta a fagen wasan Hausa, kuma ta bayyana jin daɗi game da cigaban da aka samu a harkar.
Tambaya, wadda ta ce ta fi sama da shekara 60 ta na harkar dirama, ta bayyana hakan ne a hirar musamman da ta yi da mujallar Fim a gidan ta da ke Kano.
Hajiya Tambaya, wadda ta yi fice a matsayin matar Ɗanhaki a diramar talabijin tun kafin a assasa Kannywood, ma’aikaciyar jinya ce a Asibitin Nassarawa da ke Kano, aikin da ta ce ta na yi ne domin ta tallafa wa kan ta da iyalan ta.
Tambaya ta ce daga lokacin da ta fara yin wasan kwaikwayo zuwa yanzu, masana’antar ta samu gagarumar nasara, musamman a fannin kayan aiki waɗanda su ke na zamani ne, saɓanin yadda a baya ake amfani da su kamar yadda shi kan sa ɗan’adam ya ke ci gaba zuwa ladar aiki da ake biya.
A cewar ta, “A da, dirama ma idan ka yi ba za a ba ka ko kwabo ba, amma yanzu saboda zuwan zamani kafin mutum ya fita ya yi aiki sai an gaya masa irin fitowar da zai yi, sannan kuma a gaya masa nawa za a biya shi.
“Wannan ma wani gagarumin cigaba ne kamar yadda da idan mu ka yi wannan wasan kwaikwayon ba mu da (gidan) talabijin a Kano ko ɗaya, har sai mun je Kaduna sannan ake haskawa. Wannan ma ya na ɗaya daga cikin cigaban da wannan masana’antar ta samu.”
Ta ƙara da cewa har yanzu ta na fitowa a finafinai idan an gayyace ta duk da shekarun da ta shafe a cikin wannan harka. Ta ce ‘ya’yan ta da jikokin ta, wato matasa ‘yan fim, su kan kira ta domin ta yi masu aiki.
Sannan ta bayyana jin daɗin ta game da yadda shugabannin Kannywood su ke ƙoƙarin kawo canji, musamman kan batun rashin tarbiyya da ake samu a wasu lokutan kamar yadda aka gani a kwanan nan.
Jarumar, mai shekaru kimanin 90 a duniya, ta ce mutane irin ta ba za su taɓa gudun masana’antar Kannywood ba. Ta ce ita ba ta raina sana’ar fim.
Ta ce: “Na daɗe ina yin wannan sana’ar, wanda na samu sama da shekara sittin a cikin ta. Kan wannan baiwa, ina yi wa Allah godiya.
“Duk da ba ni da arziki, ban mallaki gida ba wanda har zuwa yanzu gida ya na yi min barazana sakamakon ina zaune da marayu wanda ɗa na ya mutu ya bar min, su shida.
“Ba ni da komai, amma kuma sunan da na yi a cikin wannan masana’antar ina alfahari da shi kamar yadda al’umma su ke ƙauna ta.”
A ƙarshe, Hajiya Ladi ta yi wa masoyan ta fatan alheri tare da yin addu’ar Allah ya bar su tare.