A RANAR 9 ga Maris, 2024 Allah ya ɗauki ran Hajiya Fatima Mu’azu (Gwaggo), mahaifiyar tsohon Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu). Shekarun ta 97.
Kwana ɗaya bayan wannan babban rashi da aka yi, mujallar Fim ta tattauna da shi Afakallah domin jin irin alhanin da su ka yi na rabuwa da mahaifiya. Ya tattauna ne da HABIBU YARO HARUNA, kamar haka:
FIM: Ran ka ya daɗe, ga shi an tsinci kai cikin yanayi mara daɗi na rashin mahaifiya. Yaya ku ka ji wannan abu?
AFAKALLAHU: Alhamdu lillah. Shi tarihin marigayiya Hajiya Fatima Mu’azu, wacce ita ce mahaifiya ta, ‘ya’yan ta mu tara ta haifa amma yanzu mu takwas mu ne muke raye: akwai Tasi’u Na’abba, Abubakar Na’abba, Isma’ila Na’abba, Hafsat Na’abba, Sa’a Na’abba. Ta ɗauki shekaru kusan casa’in da bakwai a duniya.
Mace ce mai haƙuri da ibada. Mace ce mai ƙoƙarin ta ga an tsaya an bi Allah, an ga abubuwa sun tafi daidai.
Babu abin da za mu ce sai dai mu ce Allah ya ba mu haƙuri da juriya. Giɓi ne babba, amma wanda ya karɓe ta ya fi mu son ta.

FIM: Wane yanayi aka tsinci kai lokacin da aka sami labarin rasuwar?
AFAKALLAHU: To, ka san yanayi na rasuwa, balle mahaifiya, kuma da ma mahaifi mu ya rasu yau kusan shekara arba’in da bakwai, tun 1976, to ka ga an shiga maraici tun tuni. Kuma a gaban ta aka taso, duka a gaban ta aka yi gwagwarmaya. Ita ce malamar, ita ce uwa, ita ce uba, sai ‘yan’uwa da da su ke tattare da ita da su ke taimaka mana. Don haka kusan ni duk shekaru na tare da ita na yi. Amma dai yanzu babu abin da za mu ce sai dai mu yi wa Allah godiya.
FIM: Me za ka iya tunawa dangane da wani abin kirki da ya shafe ta?
AFAKALLAHU: Haƙuri. Ita mai haƙuri ce, mai kuma cewa kullum a yi haƙuri a yi abin da ya kamata. Babban abin da ba ta so shi ne rashin gaskiya. Wallahi kullum abin da za ta gaya ma kar ka ci amana, kar ku yi ha’inci, kar ku ɗauki abin da ba naku ba, lallai kar ku yi kwaɗayi, kar ka yarda ka yi kwaɗayi. Hajiya ba ta son mutum mai kwaɗayi.
Mu dai babu abin da za mu ce sai dai mu ce Allah dai ya jiƙan ta.